Kungiyar Dattawan jam’iyyar PDP na Arewa maso Gabashin Najeriya ta ce yankinsu ya fi kamata jam’iyyar ta ba takarar shugabancin Najeriya a 2023.
Kungiyar ta bayyana hakan ne ranar Litinin, a wata takadar bayan taron da ta yi, dauke da sanya hannun Dokta Aliyu Bappayo Adamu.
A cewar dattawan, muddin jam’iyyar na son lashe zabe mai zuwa, to yankinsu ya fi kamata a ba takara a jam’iyyar.
Sun yi korafin cewa rabon yankinsu da Shugabancin Kasa tun zamanin Fira-Minista Abubakar Tafawa Balewa a shekarar 1960.
Kungiyar ta ce akwai mutane da suka dace daga yankin, wadanda suka hidimta wa kasar wajen shawo kan matsalolinta, musamman a bangaren tsaro, da za a iya ba takarar.
“Shekaru da dama kudancin Najeriya ke mulkar mu domin Cif Olusegun Obasanjo, ya yi shekara takwas Goodluck Jonathan shi ma ya yi shekaru biyar, sannan Marigayi Umaru Musa ’Yar’adu’a, shi shekara uku kawai ya yi, kuma shi ba dan Arewa maso Gabas ba ne.”
Takardar ta kuma gargadi PDP da ta yi taka-tsantsan wajen tuntuba da karbar shawarin masu ruwa da tsakin da ya kamata domin ta kayar da APC a zabe mai zuwa.