✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arewa ga mafita!

Tabbas yankin arewacin Nijeriya ne ya samar da mutumin da ya yi wa kowa fintinkau a arziki a nahiyar Afirka, amma ba abin mamaki ba…

Tabbas yankin arewacin Nijeriya ne ya samar da mutumin da ya yi wa kowa fintinkau a arziki a nahiyar Afirka, amma ba abin mamaki ba ne idan aka ce wanda ya fi kowa talauci a Nahiyar Afirka a yankin yake zaune. Wannan bai zama abin mamaki ba sam idan muka yi la’akari da halin ko-in-kula da masu ruwa da tsaki na yankin suka yi bisa ga tarin kalubale da suka yi wa yankin daurin goro. Idan muka dubi matsalar
tsaro da ta yi aure ta tare a Arewa-maso-gabas, ta kuma fara barazana
ga birnin da ya fi kowane hada-hada ta fanning jama’a da kasuwanci a yankin, wato birnin Kano, da kuma matsalar rashin aikin yi a tsakanin galibin matasan yankin, ga rashin wata tsayayyar hanyar da za ta zama kafar shigowar tattalin arziki a yankin, ga matsalar rashin hadin kai a tsakanin jiga-jigan ‘yansiyasar yankin a dalilan bambamcin akida da ra’ayin siyasa, za mu iya cewa lallai an yi wa yankin sakiyar da ba ruwa.
Wadannan kalilan ne cikin tarin matsaloli da suka yi wa arewa dabaibayi, kuma suke matukar bukatar magani na gaggawa don ceto yankin daga rugujewa wanda tuni yake kan hanya. Matukar kuwa ana bukatar magance wannan tarin matsaloli, dole a samu
waddannan abubuwa da zan jero:
·  Hadin Kai Na Gaskiya A Tsakanin ‘Yan Siyasa Da Masu Fada Aji
Idan aka ce masu fada aji, wannan ya hada kowa da kowa, wato malamai da sarakuna da masana a fannoni daban-daban da sauran su, Ina tuna wani abin da ya burge ni a kwana-kwanan nan da ya faru a kasar Birtaniya, a lokacin da yankin Scotland ya yi yunkurin ballewa daga Birtaniya, duniya ta ga yadda Fira Ministan Birtaniya, Dabid Cameron ya yi iya kokarinsa don ganin tabbatar da wannan yunkuri bai kai ga nasara ba, muna sane da yadda hatta ‘yan adawa a majalisar da Cameron ke jagoranta suka yi namijin kokari wajen dakile wannan yunkuri saboda tunanin makomarsu matukar Scotland ta balle. Babban abin da ya dauki hankalin duniya da ‘yan jarida gami da masu bibiyar lamuran yau da kullum shi ne, yadda Fira Minista da shugaban ‘yan adawa a wannan majalisa suka mance da
duk wata adawar da ke tsakanin su, suka fuskanci kalubalen da yake kokarin auka wa kasarsu, suka magance wannan matsalar, sannan hankalinsu ya kai ga kwanciya. Wannan duk sun yi saboda hangen nesa ga makomar su da kuma kishin yanki ba tare da kawo batun jam’iya ko ra’ayi ba. Shin ‘yan siyasarmu na arewa suna kwatanta wannan yunkuri don magance mafi munin kalubale da yankinsu ke fuskanta ? Amsar a nan ita ce a’a, domin a maimakon haka, galibin ‘yan siyasarmu suna la’akari ne da abin da zai kai ga aljihunsa ko da kuwa wane hali yankinsu ka iya shiga. Kenan idan an samu hadin kai da matsalolin yankinmu ba su kai haka ba. Saboda haka a mataki na farko, sai an sami hadin kai a tsakanin ‘yan siyasa, shugabannin addinai, sarakuna da masana sannan za a sami fahimtar da za ta kai mu ga fuskantar manyan tarin matsaloli da suka addabe mu, sa’annan mu kuma iya magance su cikin gaggawa.
· Talakawa Su Kasance Masu Biyayya Ga Shuwagabanni:
Idan har kawunan magabata ya kasance a hade, babu wata baraka, sannam talakawa a bangarensu suka kasance masu mara musu baya a duk wani yunkuri da
suke yi ta hanyar yin biyayya ga duk wata shawara da suka cimma, to hakika an fara dosar tudun tsira, domin kowa na ganin mutuncin kowa. Tambayar da zan yi ita ce  shin a yanzu an samu wannan alaka tsakanin shugabanni da talakawan arewa ? Amsar a nan ma ita ce, a’a, domin yawancin talakawan arewa na zargin wasu manya cikin shugabannin yankin da hannu a mummunan yanayin da yankin ke ciki, wannan abu ne da yake a bayyane. Don haka akwai bukatar duba wannan matsala a kuma bi matakin gaggawa da ya dace.
Wani babban abin da yake damu na yanzu shi ne, yadda shugabanninmu na arewa suka yi watsi da tabbataccen arziki wato noma da kiwo, a dalilin samun man fetur wanda bai da tabbas, hakan kuma ya yi mummunar shafar kimarmu a idan takwarorinmu na kudu, matukar za mu juya akalar
tunaninmu ya zuwa bunkasa noma da kiwo, da mun kama hanyar kawo karshen cin fuska da al’ummar kudu ke mana, inda suke kiran mu da kaska, shin kasashe nawa ne suke dogaro da man fetur a duniya yanzu? Idan aka yi nazari za a ga ba su da yawa, su ne ‘yan kadan. Sannan kasashe nawa ne suke rayuwa cikin kwanciyar hankali da rayuwa cike da walwala ba tare da suna da man fetur ba illa dogarar da suka yi a kan noma?
Saboda haka zan yi amfani da wannan dama wajen jaddada wa gwamnonim arewa wata shawara da wani Farfesa ya ba su a wani taro da suka gudanar a baya, matukar arewa na bukatar dawo da kimarta, to ya zama dole ta gudanar da wani shiri mai kama da adashe, misali kowane wata ya kasance suna tara miliyan dari-dari daga kowace jiha, sannan a ba da wannan kudi ga jiha gudu a kuma nemi fanni guda na rayuwa ko wani abu da wannan jihar ta kware wajen samar wa, a yi amfani da wannan kudi wajen tabbatar da bunkasa wannan abin, sannan kuma ya kasance sauran jihohin arewa, ba inda za su je su siya irin wannan abin, sai a jihar nan, ita kuwa jihar ya zama ba za ta taba sayar da wannan kaya ga wata kasa ba sai a wata jihar arewa, haka za a dinga yi a tsakanin jihohi, wannan zai taimaka wajen samar wa dubban matasa aiki, ga kuma samar da kudin shiga mai yawa da albarka.
Hakika idan za a jarraba wannan shawara, to nan da shekara daya zuwa biyu za a sha mamaki, domin za a iya amfani da moriyar da ake.samu wajen bunkasa noma a kuma iya fara hako man fetur a wasu yankuna tunda akwai man fetur mai yawa a arewa.
Ina fatan wadannan shawarwari da na gabatar a matsayi na dan karamin dalibi, za su taimaka. Allah Ya daukaka mana arewa, ya kuma ba mu ilmin da za mu iya yakar matsalolin da suka mana kawanya, mu samu zaman lafiya da
kwanciyar hankali su dawo kamar a shekarun baya. Ameen.

Daga Usman Bin-Affan Damaturu
Sakataren kungiyar zabi sonka, kana jami’i a kungiyar muryar talaka a karamar Hukumar Damaturu.