✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Arewa ake neman karyawa da zanga-zangar #EndSARS —Sheikh Jingir

Akwai siyasa a ciki, shi ya sa muke kira ga jama'a da su nisance shi

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya zargi masu zanga-zangar #EndSARS da neman karya Arewacin Najeriya.

Babban malamin ya bayyana zargin haka ne a lokacin da yake jawabi a hudubar sallar Juma’a a garin Jos, Jihar Filato.

Malamin kungiyar ta izala, ya ce zanga-zangar #EndSARS wani shiri ne na kassara Gwamantin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma yankin da ya fito.

Da yake kwatanta yawancin masu zanga-zangar da ‘yan daba, malamin ya kuma zarge su da fakewa ne da zanga-zangar domin cimma manufar tasu.

“Babu ruwanmu da zanga-zangar #EndSARS saboda babu tsarkin niyya a cikinsa.

“Muna kiran jama’a da su nisance shi.

“Akwai siyasa a ciki, shi ya sa muke kira ga jama’a da su nisance shi.

“Abin da muke bukata yanzu shi ne addu’o’i domin samun cigaban kasa da kuma magance matsalar tsaro da ke addabar al’ummomi”, inji shi.

Shehin malamin ya kuma yi kira ga Shugaba Buhari da ya gaggauta daukar mataki a kan lamarin masu zanga-zangar tun kafin abin ya gagari kundila.