✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arangamar sojoji da ’yan kungiyar IPOB: An kafa dokar- ta-baci a jihar Abia

Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya kafa dokar-ta-baci ta kwanaki uku a jihar yayin da hankula suka tashi sakamakon arangamar da aka yi tsakanin sojoji…

Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya kafa dokar-ta-baci ta kwanaki uku a jihar yayin da hankula suka tashi sakamakon arangamar da aka yi tsakanin sojoji da ’yan kungiyar IPOB masu rajin kafa kasar Biyafara.
Dokar-ta-bacin ta fara ne daga yau karfe shida na safe zuwa karfe shida na yamma har zuwa ranar juma’a mai zuwa.
Ikpeazu ne ya sanar da dokar-ta-bacin jiya, a gidan gwamnatin jihar yayin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan taron majalisar tsaron jihar da shugabannin hukumomin tsaron jihar.
Gwamnan ya jaddada kudurinsa na kare kundin tsarin dokokin Najeriya sannan kuma ya bayar da tabbacin hada kai da gwamnati don kawo karshen masu son ballewa daga Najeriya.
Ya bayyana cewa sojojin da sauran jami’an tsaron Najeriya suna da ikon yin duk abin da dokar kasa ta basu damar yi.
To sai dai kuma ya bukace su da su girmama hakkin al’ummar jihar tare da kare rayukansu.