A ranar Talata ake sa ran Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, zai kaddamar da manhajar da ya kirkiro don neman tallafin kudi daga hannun ’yan Najeriya.
Kwamitin ya ce ya kirkiro manhajar ‘Crowdfund’ ne don tara kudaden da zai yi amfani da su wajen tallata dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima.
- NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilin Ci Gaban Wahalar Mai —Masani
- Kotu ta tabbatar wa Machina takarar Sanatan Yobe ta Arewa
Sanarwar da kwamtin ya fitar ta ce manhajar za ta bai wa ’yan Najeriya damar mika gudunmawarsu don mara wa Tinubu/Shettima baya.
A cewar Kwamitin, manhajar za ta taimaka wajen takaita mu’amala da tsabar kudi a harkokin zaben 2023.
Wannan shi ne kwatankwacin abin da ya faru yayin yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari a wa’adinsa na farko, inda aka kirkiro da katin waya da ya bai wa talakawan kasa damar mika gudunmawarsu ga neman zabensa.