✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta shiga ruɗani a Zamfara

Mambobin APC sun fada cikin rikicin shugabanci, tsawon mako biyu suna dambarwa.

Jam’iyyar APC mai adawa a Jihar Zamfara ta fada cikin rudani kan yadda tafiyar jam’iyyar ke gudana, inda mambobi da shugabanninta suka fada cikin rikicin shugabanci, tsawon mako biyu suna dambarwa.

Rikicin ya faro ne a ranar Asabar din makon jiya, inda shugabannin Jam’iyyar APC a Mazabar Galadima a Karamar Hukumar Gusau suka bayyana korar shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Tukur Danfulani kan zargin rashin kwarewa a shugabancin jam’iyya.

A hirar shugabannin da manema labarai a Gusau sun ce, sun yanke hukuncin ne domin a ceto jam’iyya daga bakin mulkinsa.

Mataimakin Shugaba a mazabar da Shugaban Jam’iyyar ya fito, Alhaji Garba Bello ya ce, shugabanni 16 daga cikin 27 sun sanya hannu tare da amincewa da korar Tukur Danfulani daga jam’iyyar.

A cewar Alhaji Garba, kashi 90 na shugabannin jam’iyya ba sa tare da Danfulani hakan ya sa jam’iyyar ta rabu gida biyu, inda ya yi kira ga uwar Jam’iyyar APC ta Kasa, ta samar da shugabannin rikon kwarya a jihar.

Bayan wannan ne, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, Yusuf Idris ya fitar da wata takarda ga manema labarai cewa, maganar korar shugaban ba gaskiya ba ce.

Ya ce wasu ne kawai da ke kiran kansu shugabannin mazabar Danfulani suka kitsa lamarin kuma ba za su yi nasara ba. Don haka kada mutane su kula da shirmensu.

Ya ce, jam’iyyar tana sane da ’yan siyasar da ke kokarin kawo hatsaniya a cikinta a shirinsu na kafa sabuwar jam’iyya don zaben 2027, wanda hakan suka yi a Kano da wasu jihohi.

Saboda haka, mummunar manufarsu ba za ta yi nasara ba. Sakataren ya ce, in wasu mambobin jam’iyyar na da matsala da shugaba, akwai hanyoyin da ake bi don warware komai a tsanake ba tare da rigima ba.

Kwana ɗaya da haka sai shugabanni takwas daga cikin 16 da suka kori shugaban suka zo hedikwatar jam’iyyar suka ce, sun janye sa-hannun da suka yi kan cire Danfulani domin yaudararsu aka yi, su sun gamsu da shugabancin Danfulanin.

Sakataren Jam’iyyar, Ibrahim Umar Daangaladima da ya karbi takardar goyon bayan da suka kawo, ya ce, wadanda suke son cire shugaban ba su bi ka’ida ba, domin jam’iyya na da dokoki.

Ana cikin wannan dambarwar ranar Juma’ar da ta gabata Jam’iyyar APC a matakin jiha ta bayar da sanarwar dakatar da Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar kananan hukumomin Birnin Magaji da Kauran Namoda, Alhaji Aminu Sani Jaji daga jam’iyyar saboda zarginsa da yi wa jam’iyyar zagon-kasa da raba ta gida biyu da sanya ’ya’yan jam’iyya rashin aminta da juna.

Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar APC na Jihar, Yusuf Idris ne ya karanta dakatarwar bayan shugabannin jam’iyyar sun karbi takardar koke da dakatarwar daga mazabar dan majalisar.

A yayin zantawa ta wayar tarho da ɗaya daga cikin makusatan ɗan majalisar, Malam Abdulmunafi Usman ya bayyana Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Alhaji Tukur Umar Ɗanfulani a matsayin tsintacciyar mage wadda ba ta mage.

Malam Abdulmunafi Usman yana tsokaci ne a kan korar da ake yaɗawa cewa an yi wa mai gidansu, Aminu Sani Jaji daga Jam’iyyar APC, inda ya ce, korarren shugaban jam’iyya ba zai iya jagorantar korar wani ɗan jam’iyya ba.

Ya ce wasu tsiraru ne kawai marasa aikin yi da suke neman na abinci aka yi amfani da su domin su ɓata wa mai gidansu suna.

Wasu na zargin yaran tsohon Gwamna Ahmad Yarima ne da na tsohon Gwamna Bello Matawalle suke rigimar neman shugabancin jam’iyyar a jihar, inda suke haddasa wannan rudani.