Sakamakon zaben Kananan Hukumomin da aka gudanar a Jihar Katsina ranar Litinin ya nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki ta lashe kujerun Ciyamomi 31 daga cikin 34 da ake da su a Jihar.
APC ta yi nasara ne a zaben, wanda aka yi a duk fadin Jihar ranar Litinin.
Sai dai har yanzu ana dakon sakamakon Kananan Hukumomin Funtuwa kuma Daura, mahaifar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Kazalika, Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Jihar ta soke sakamakon Karamar Hukumar Dutsinma saboda wasu dalilai, kamar yadda Sakataren hukumar, Alhaji Lawal Alasan Faskari, ya shaida wa manema labarai a daren Litinin.
Sakataren, har ila yau, ya ce, baya ga lashe kujerun shuwagabannin Kananan Hukumomin da APC ta yi, har ila yau, ta kuma lashe na kansilolin da aka ayyana sakamakonsu.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, ba a samu sakamakon ragowar Kananan Hukumomi biyun ba.
Hukumar zaben ta kuma ce nan gaba za ta bayyana ranar da za a sake zaben Karamar Hukumar Dutsinma.
Ana iya cewa zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wani tashin hankali ko farmakin ’yan bindiga ba kasancewar Jihar na fama da matsalar tsaro.
Sai dai a wasu wuraren an sami matsaloli kamar na kai kayan zabe a makare da rashin samun wasu takardun yadda ya kamata, sannan wasu matasa sun kone kayan zabe a Karamar Hukumar Bakori.
Bugu da kari, duk da cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta bayar da sanarwar takaita zirga-zirgar ababen hawa, hakan bai hana jama’a ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba.