✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC Akida PDP take yi wa aiki, Inji Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana membobin  APC Akida a matsayin wani bangaren adawa na jam’iyyar APC da ke yi wa PDP aiki…

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana membobin  APC Akida a matsayin wani bangaren adawa na jam’iyyar APC da ke yi wa PDP aiki don ruguza jam’iyyar APC.
Masari ya ce an kafa kungiyar ne don a ruguza siyasar Buhari inda ya yi zargin cewa kungiyar tana yi wa jam’iyyar adawa ta PDP ne kawai.
Ya ce “Ba ni ne wanda kungiyar ke nufi ba, sun sanya ni ciki ne kasancewata gwanan jihar da Buhari ya fito amma a zahiri Buhari ne manufarsu”.