✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Anya kuwa tafiyar Al-Mustapha da su Dokubo ba tafiyar kare da kure ba ce?

Tun ranar Juma`a 12 ga watan Yulin da ya gabata da Manjo Hamza Al-Mustapha, dogarin tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha ya samu `yancin…

Tun ranar Juma`a 12 ga watan Yulin da ya gabata da Manjo Hamza Al-Mustapha, dogarin tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha ya samu `yancin kansa, bisa ga hukuncin da Kotun daukaka kara ta Legas ta wanke shi a cikin tuhumar zargin kisan uwargida Kudirat Abiola, bayan ya shekara sama da 14, yana garkame. Manjo Al-Mustapha tare da rakiyar wasu aminai da abokai da `yan uwa da wasu kungiyoyin matasan Arewacin kasar nan, suke ta kai ziyara ganawa da godiya ga jama`ar sassa daban-daban na kasar nan. Ziyarar da ya fara tun daga Legas, inda ya sha dogon zaman jiran shari`ah.
 Tun a Legas ya ziyarci shugaban dayan bangaren kungiyar nan ta `yan kabilar Yarbawa zalla, ta Oduduwa wato OPC, ta  Dokta Fredrick Fasheun, sannan kuma ya ziyarci Fasto Tunde Bakare, wanda ya rufa wa Janar Muhammadu Buhari baya a cikin takarar neman shugabancin kasar nan a zaben shekarar 2011, a inuwar rusashshiyar jam`iyyar CPC, wadanda duk ya ce tun yana kan karagar mulki da kuma duk tsawon lokacin da yake tsare, yana da kyakykyawar alaka da su.
    A nan Arewa kuwa, wasu daga cikin garuruwan da Manjo Al-Mustapha da ayarin nasa suka kai ziyara sun hada da birnin Kano, inda nan yake da zama da mahaifansa kafin Allah Ya yi masu rasuwa cikin yana tsare da garuruwan Damaturu, babban birnin jihar Yobe, jiharsa ta asali da garin Nguru wanda shi ne mahaifarsa da Gashuwa, ya kuma ziyarci Kaduna garin gwamna da sauran wasu garuruwa na jihohin Arewa.
A duk inda ya je a cikin wadancan ziyarce-ziyarce, an ta sha jin Manjo Al-Mustapha ya kan ce ya yafe wa dukkan wani ko wasu da ake zargin su suka yi sanadiyyar zamansa na gidan Yari, yakan kara da cewa kaddara ta Allah ce ta same shi, kuma yana fata ta zame masa kaffara.
  Mai karatu tsawon tsarewar da aka yi wa Manjo Al-Mustapha, wadda wasu ke bayyanata da cewa ita ce ta farko irinta da aka taba yi wa wani babban mutum a kasar nan akan laifin da ake zargin ya danganci siyasa, shi ya janyo masa samun tausayawa ga dukkan wani dan Arewa musulmi na ciki da wajen kasar nan, haka kuma ya kara jefa kiyayya tsakanin `yan Arewa da `yan kabilar Yarbawa, bisa ga irin yadda shari`ar ta-ki-ci-ta-ki-cinyewa, har ta kai fagen duk wani da ya isa a Arewa sai da ya roki Gwamnatin Jihar Legas da ta yi wa Allah ta duba shari`ar nan da idon rahama ta sa a kare ta, ko Al-Mustapha ya san makomarsa, amma gwamnatin ta ce ba ruwanta sai lokacin da shari`ah ta yanke hukunci.
Fitowar Manjo Al-Mustapha ke da wuya sai wasu matasa a karkashin kungiyoyinsu daga nan Arewa, suka rika kwatanta shi da shugaban kasar Afirka ta kudu na farko a jerin shugabannin bakar fata wato Dokta Nelson Mandela, a zaman dan gwagwarmaya, har ta kai suna kiraye-kirayen lalle sai ya fito takarar neman shugabncin kasar nan a shekarar 2015. Masu fadin haka ban sa ni ba da gaske suke ko koda gangaan koda ganganci?
A yanzu maganar da ake ciki a ranar 12 ga wannan watan Manjo Al—Mustapha ya kai wata ziyara a jihohin Imo da Anambra da ke shiyyar Kudu maso Gabas, inda a can suka hadu da mutane, irinsu Alhaji Mujahid Asari Dokubo da Dokta Fredrick Fasheun da Cif Uwazuruike, inda suka tattauna ya junansu a zaman shugabannin kungiyoyin matasa na sassa daban-daban na kasar nan, da zummar samun hadin kan matasan kasa. Sannan suka kai ziyara ga wasu Sarakunan gargajiya da jihohin biyu, amma abin tambaya akan aniyarsa ta yin tafiya tare da wadancan shugabanni uku, ita ce kuwa abokan tafiyar Manjo Al-Mustapha ne da har za su hadu da aniyar cimma wata manufa, har su iya biyan bukatun sauran alummar kasa?
 `Yan kasa dai sun san cewa Alhaji Dokudo, kafin shekarar 2010, da marigayi shugaban kasa Alhaji Umaru Musa `Yar`aduduwa ya yi tayin afuwa ga tsagerun yankin Neja Delta, sunyi kaurin suna wajen fasa bututun man fetur don satar man da kuma yin garkuwa da mutane, musamman `yan kasashen waje don neman makudan kudi da sunan fansa, shi ne shugaban daya daga cikin shugabannin irin wadancan kungiyoyi, sunan kungiyarsa kungiyar sa kai mai aiki da karfi ta Neja Delta wato NDbF, ko a kwanan nan an ji shi yana barazanar cewa muddin shugaban kasa Dokta Goodlluck Jonathan, ya fadi zaben 2015, to, kuwa za a zubar da jini a kasar nan. Allah Ya kiyaye.
 Shi kuwa Dokta Feshuen shi ya kirkiri kungiyar `yan kabilar Yarbawa ta OPC, duk da yake bangarensa baya da tsatstsauran ra`ayin daukar makamai, amma dai dayan bangaren da Mista Ganiyu Adams yake jagoranta ya yi kaurin suna wajen yawan kashe `yan Arewa da suke kasar Yarbawa a shekarun baya.
Shi kuwa Cif Uwazuruike, an sha kama shi har ana daurewa,  bisa fafutikar da har gobe yake kai a karkashin kungiyarsu ta tabbatar da `yancin kasar Biyafara, wato MASSOB, kasar da marigayi Laftanar Kanar Odumegwu Ojukwu madugun `yan tawaye ya kafa a shekarar 1966, a zamanin da `yan kabilarsa ta Ibo suka yi yunkurin ballewa daga tarayyar kasar nan, amma aka yake shi har watanni 30.
 Shi kuwa Manjo Al-Mustapha kowa ya san cewa duk tsawon rayuwarsa ta sama da shekaru 50, bai san kome ba sai aikin soja, shi kuwa aikin soja daya daga cikin  tarbiyarsa ita ce dora son kasa fiye da kome, don haka ina tafiyarsa zata yiwu da mutanen da suke da dabi`ar tawaye da neman a kawo wa kasa rashin zaman lafiya don kawai son kabilarsu. Wannan tafiya ce dai kawai da za a kira ta ta “kare da kura”, wadda kowa ya san cewa ba za a kwashe lafiya ba. Ni ina daga cikin mutanen da suke ba Manjo Al-Mustapha shawarar da ya saurara har ya kara fanimtar dawan garin. Ya kamata ya sa ni daga shekara 15, da suka bar mulki zuwa yanzu abubuwa sun mugun canjawa, ta yadda daga fari sun rikide sun zama bakikkirin, wadanda shi ina jin har yanzu fari yake ganinsu.