Tun bayan bayyanar wasikar nan mai shafuffuka 18, a ranar Laraba 4 ga wannan watan a bainar jama`a da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wa shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, mai taken “Kafin a makara,” wadda a ciki ya zargi shugaba Jonathan da batutuwan da suka kunshi mulkin kabilanci da kasa tabuka kome akan yaki da cin hanci da rashawa da kuma kasa shawo kan tabarbarewar matakan tsaro na rikicin Boko Haram da shiyyar Arewa maso Gabas da wasu jihohin Arewa suke fama da su da na yankin Neja-Delta na sace mutane da yin garkuwa da su da neman kudaden fansa da kwadayin sai ya ci gaba da mulki a shekarar 2015, alhali ya yi alkawari a shekarar 2011, cewa sau daya zai yi mulki.
A cikin wannan hali aka shiga cacar baki tsakanin wadanda suke gayan bayan zarge-zargen da wasikar ta Cif Obasanjo ta kunsa da kuma masu goyon bayan shugaba Jonathan. Yayin da masu goyon bayan wasikar, suke ta kiraye-kirayen lallai sai Shugaba Jonathan ya fito ya kare kansa, har ma masu wannan ra`ayi suka rika kiran `yan Majalisun Dokoki na kasa su bi sawun waccan wasika da aniyyar su dauki matakan da za su tsige Shugaba Jonathan, muddin suka tabbatar da zarge-zargen. Su kuwa masu goyon bayan Shugaba Jonathan da shi kansa, suna can sun dukufa haikan wajen bullo da matakai daban-daban da aniyar ganin lallai sai shugaba Jonathan ya ci gaba da mulki a shekarar 2015.
Zuwa yanzu Shugaba Jonathan ya yi ta maza, inda ya yunkura, a ranar 20 ga wannan watan ya aike wa Cif Onasanjo amsar waccan wasika, inda ya bayyana Cif Onasanjo da cewar so kawai yake ya damalmala matakan tsaron kasar nan, sannan kuma a gefe daya ya zuga `yan kasar nan, ya kara da cewa don kuwa ko ba kome a zaman Cif Obasanjo tsohon shugaban kasa da ya mulki kasar nan shekaru kusan 12 (a zaman shugaban kasa na soja da farar hula), ya san dukkan irin abubuwan da suke gudana a cikin harkokin gudanar da mulki, don haka kamata ya yi idan ma zai wage bakinsa akan harkokin kasa, to, ya san irin maganar da zai fadi. Amma kuma duk da martanin shugaba Jonathan din, da ya kunshi kalmomi 4,984, ba inda ya musanta zargin da tsohon shugaban kasar ya yi masa na cewa, ba abin da ke gabansa illa yadda zai ci gaba da mulki, bayan shekarar 2015.
A gefe daya su kuma sojojin baka na Shugaba Jonathan suna can sun dukufa wajen ganin lallai sai shugaba Jonathan ya koma kan karagar mulki a shekarar 2015, kamar yadda yanzu ya fito fili a labarin da yayar wannan jaridar, wato Weekly ta ranar 22-12-13, (ta karshen makon da ya gabata), ta dauko a shafinta na farko mai fassara kamar haka- “2015: `Yan Arewa 151 da za a tuntuba don Jonathan.” Jerin sunayen mutanen da wani kundi da jaridar ta kwakwulo, jaridar ta ce za a tuntubesu don neman amincewa da goyon bayansu akan takarar shugaba Jonathanta a 2015. Jaridar, ta fadi cewa, wani babban dan siyasa kuma dan asalin jihar Bauchi, shi wai ya zakulo mutanen, wadanda suka kunshi `yan siyasa da dattawa kasar nan da tsofaffin hafsoshin sojoji da na `yan sanda da Sarakuna da `yan boko da shahararrun`yan kasuwa da wasu mata biyu a jerin sunayen, wato Hajiya Naja`atu Mohammad da Helen Gomwalk matar tsohon gwamnan mulkin soja na Jihar Binuwai da Filato marigayi Kwamishinan `yan sanda Dabid Deshi Gomwalk..
A kwanakin baya wajen bikin cika shekarau 25, akan karagar mulki na mai martaba Sarkin Minna, Alhaji Umaru Bahago da gwamnan Jihar Neja Dokta, Ma`azu Babangida Aliyu ya yi zargin cewar gwmantin Dokta Jonathan ta tsara sunayen `yan Arewar da za ta tuntuba don neman taimako da goyon bayansu akan takarar shugaban kasar ta shekarar 2015, in Allah Ya kaimu. Yanzu kuma maganar da ake tuni wadancan sojojin baka sun fara kai ziyarar neman wannan goyon baya ya kai ziyarar saduwa da mutanen da ya tsara na jihar Neja.
Rashin fili a wannan makala ba zai bani damar kawo jerin sunayen mutanen da wancan kundi ya kunsa, amma dai zai yi kokarin kawo yawan na kowace jiha da wasu daga cikin mutanen da suka saukaka. Jihar Adamawa ke kan gaba da mutane 15, sai jihohin Katsina da Kabbi masu mutane sha hurhudu, sai jihar Kano mai mutane sha 11, jihohin Barno da Jigawa suna da mutane goma-goma, yayin da akwai mutane tara-tara daga jihohin Binuwai da Filato, jihar Bauchi na da mutane 8. Sauran jihohin da mutanensu da sojojin bakan na shugaba Jonathan suka zaba don marawa tafiyarsa ta 2015, sun hada da jihohin Kaduna da Kogi masu matane bakwai-bakwai, jihohin irinsu Kwara da Sakkwato da Taraba, suna da shidda-shidda, Jihohi masu mutane biyar-biyar sun hada da Neja da Zamfara da Yobe, yayin da jihar Nassarawa take da mafi kankantan mutane hudu.
A jerin mutane kuwa, in ji binciken jaridar Weekly Trust din,akwai muatnen da hankali ba zai amince da koda an gayyacesu za su amsa gayyatar bare su amince su shiga jirgin shugaba Jonathan din. Mutane irinsu Farfesa Ango Abdullahi da Dokta Junaidu Muhammad da Alhaji Isyaku Ibrahim da Cif Paul Unongo da Dokta Usman Bugaje da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, bisa ga irin matsayinsu da aka sa ni na adawa da mulkin shugaba Jonathan, da kalamansu a bainar jama`a na lallai sai shugaba Jonathan ya bar mulki a shekarar 2015, ba a tsammanin su mara wa tafiyar baya. Akwai kuma mutane irinsu Farfesa Sanata Jibril Aminu da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sanata Saminu Turaki da Janar T. Y. Danjuma da Kanar dangiwa Umar da Alhaji Tanko Yakasai, ko dai a kan siyasar da ake yi a jihohinsu ba a yi da su ko bisa ga irin jawaban da suka furta na nuna adawa da waccan takarda da tsohon shugaban kasa Cif Obasanjo ya rubuta wa shugaba Jonathan, ana kallon za su mara wa tafiyar baya.
Masu iya magana kan ce “Ra`ayi riga,” don haka da wadanda suka amsa wannan gayyata da wadanda suka ki, bisa ga `yancin da suke da shi ba wanda ya yi wa kasa laifi, sai dai ko a ce mutanensa. Amma dai abin da kullum yake kara bayyana yayin da ake karato shekarar jajibirin zabubbukan 2015, shi ne lallai Shugaba Jonathan yana son ko ta halin kaka ya zarce da mulki bayan 2015. Da wannan ba abin da ya rage wa dukkan mai hankali a kasar nan da ya wuce dukufa kan yin addu`a ta Allah Ya sa a yi zabubbukan lami lafiya, Ya kuma bada ikon zaben shugabannin da za su tausaya wa talakawa, ta hanyar gudanar da mulkin kwatanta gaskiya da adalci.
Aniyar Tazarcen Shugaba Jonathan ta bayyana
Tun bayan bayyanar wasikar nan mai shafuffuka 18, a ranar Laraba 4 ga wannan watan a bainar jama`a da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo…