✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargi ‘yan sanda da kashe matashi a Sakkwato

Ana zargin ’yan sanda da kashe wani matashi dan shekara 22 a wurin tarzomar da ta barke a tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da PDP…

Ana zargin ’yan sanda da kashe wani matashi dan shekara 22 a wurin tarzomar da ta barke a tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da PDP a ranar Asabar da ta gabata a Unguwar Gawon Nama da ke Sakkwato.

Marigayin mai suna Imrana Ahmad Alkanci an harbe shi ne a kirji lokacin tarzomar.

Wata majiya ta ce abin da ya haifar da tarzomar shi ne wadansu matasa magoya bayan APC sun yi yunkurin hana ayarin Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal wucewa ta titin Gawon Nama inda gidan jagoran Jam’iyyar a Jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko yake.

Gwamnan wanda ya dawo gida a ranar, magoya bayansa sun tarbo shi a filin jirgin sama na Abubakar III bayan ya dawo daga zaben fid da gwani na takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP a Fatakwal.

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa, “A ranar akwai daurin aure da aka yi gidan Sanatan, Area Boys suna gidan inda suka  sha alwashin ba wani dan PDP da zai wuce ta gaban gidan, a haka duk wanda ya zo sai sun mayar da sh. Bayan Gwamna ya shigo gari ya biyo ta hanyar sai suka tari ayarin don hana su wucewa, inda kafin a ankara wurin ya turnuke har wani ya dauko dutse ya jefi motar Gwamna su kuma ’yan sanda sai suka yi harbi, ya fada kan wanda bai ji ba, bai gani ba. Daga nan ne aka rika watsa barkono mai sa hawaye har aka samu hanya kowa ya rika wucewa,” inji shi.

Dan uwan marigayin, kuma Jami’in Hulda da Jama’a na Jami’ar Jihar Sakkwato, Zayyanu Shehu ya tabbatar wa Aminiya rasuwar matashn, ya  kara da cewa matashin yana tsaye ne zai tari acaba ya hau don tafiya gida, bayan baro gidan dan uwansa a unguwar sai harbin ya same shi, inda kuma a nan take ya rasa ransa.

Ya ce an yi masa sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kuma tuni Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya yi wa iyalan mmacin  gaisuwar ta’aziya.

Kakakin Hukumar ’Yan sandan Jihar, Cordelia Nwewe ta ce ana bincike kan lamarin, kuma za a sanar da manema labarai in bukatar hakan ta taso.