✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana kasuwanci da matsalar tsaro a Najeriya – Solomon Dalung

Barista Solomon Dalung jigo ne a kungiyar Dattawan Arewa kuma dan gwagwarmayar kare hakkin dan Adam a Najeriya. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana da…

Barista Solomon DalungBarista Solomon Dalung jigo ne a kungiyar Dattawan Arewa kuma dan gwagwarmayar kare hakkin dan Adam a Najeriya. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana da dalilin da suka sa aka kasa magance matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya. Kuma ya yi bayani kan halayen ’yan siyasar Najeriya da kuma ikirarin da Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi cewa za ta gudanar da zabe na adalci a badi:

Aminiya: Me za ka ce dangane da yadda harkokin tsaro ke kara tabarbarewa a kasar nan?
Solomon Dalung: An dade ana maganar tabarbarewar harkokin tsaro a kasar nan tare da bayar da shawarwari kan hanyoyin da za a bi a magance matsalar. Amma har yanzu ba a samu saukin matsalar ba. Wannan al’amari ya danganta ne da yadda hukuma take daukar shawarwarin da ake bayarwa kan hanyoyin magance wannan matsala. Saboda haka yanzu abin ya kai wani yanayi na ban tsoro da damuwa kwarai da gaske, kowane mutum mai hankali ya damu. A gaskiya al’amarni yana da matukar ban tsaro da tausayi.
Aminiya: To, me kake ganin ya sanya aka kasa shawo kan wannan matsala ta tsaro a kasar nan?
Solomon Dalung: An kyale wannan matsala ne tunda farko, domin ba a yi zaton za ta zama haka ba. Maimakon a tunkari wannan matsala tun da farko, sai aka shigar da siyasa a cikinta. Shugaban kasa maimakon ya dauka cewa hari ne aka kawo wa kasar nan, ya tashi nemi hadin kan ’yan kasa domin a fuskanci matsalar. Sai aka shigar da siyasa aka ce mutanen Arewa ne suke wannan abin, domin sun rabu da mulki. Wannan shigar da siyasa a cikin wannan al’amari na matsalar tsaro shi ne ya kawo mu ga wannan hali da muke ciki a yau a kasar nan. Domin da zarar ka sanya siyasa a cikin matsalar tsaro to shi ke nan, zai zama kamar kasuwanci. To abin da yake faruwa ke nan a kan wannan al’amari.
Aminiya: Ganin yadda abubuwa suke tafiya yanzu a kasar nan, mene ne hasashenka game da zabubbuka masu zuwa badi?
Solomon Dalung: Yana da wuya mutum ya fadi wani abu kan yadda zabubbukan badi za su kasance. Domin sau da yawa a kasar nan, abubuwa sukan lalace kamar haka amma sai a zo lokacin zabe sai ’yan siyasar da suke yan ta domin cika aljihunsu, ba domin ci gaban kasa ba, su dawo da hankalinsu ga hadin kai domin a samu a yi satar kuri’a a kafa gwamnati saboda su samu rabonsu. Don haka wai mutum ya yi bayani kan abin da zai faru nan gaba a kasar nan game da zabe ganin halin ‘yan siyasar Najeriya yana da wuya a wurina. Domin ’yan siyasar Najeriya sun fara nuna halayensu da suka saba, saboda wadanda suka kafa wata jam’iyya idan aka ba su kudi, sai ka ji yau sun canja sheka sun koma wata jam’iyyar. Wasu ma su ne suka shugabanci hada wata sabuwar jam’iyya an zo tun kafin a yi zaben shugabannin wannan jam’iyya, suka fice suka ce ba za a yi masu adalci ba. Saboda haka halayen ’yan siyasar Najeriya yana da wuya mutum ya ce ga yadda zabubbuka za su kasance a badi.
Aminiya: Ka gamsu da ikirarin da Hukumar INEC ta yi cewa za ta gudanar da zabe na adalci a badi?
Solomon Dalung: A kowanne lokaci haka suke fada, saboda haka muna so mu gani a kasa kan wannan ikirari nasu.
Aminiya: Me za ka ce kan yadda Gwamnatin Tarayya ta nuna adawa da sabon Sarkin Kano da aka nada?
Solomon Dalung: Bisa ga dokar nada Sarkin Kano gwamnatin Jihar Kano ce take da hakkin nada shi, bayan ta karbi rahoto daga majalisar masu zaben sabon Sarki. Tun ba a je ko’ina ba sai muka ji Jam’iyyar PDP ta kasa ta fito tana aika sakon taya murna ga wani cewa wai shi ne sabon Sarki. Ya kamata a ji sanarwar sabon Sarki daga gwamnatin Jihar Kano, kafin PDP ta aika da wannan sakon taya murna. Amma sai suka yi riga malam masallaci. Wannan ba daidai ba ne, wannan cin fuska ne ga tsarin mulkin Najeriya da dimokuradiyya kuma neman tada fitina ne a kasar nan. Kuma irin wadannan abubuwa ne suka haifar da rigingimun da muke fama da su a kasar nan a halin yanzu. Wato gwamnatin Najeriya tana aikata abubuwan da ba su dace ba, wadanda ba sa kan tsari na dokar Najeriya. Irin wadannan abubuwa da gwamnatin Najeriya take aikatawa za su ci gaba da jefa ta a cikin kunya kamar yadda ta ji a wannan nadi na sabon Sarkin Kano.
Aminiya: To, wane sako ko kira ne kake da shi ga al’ummar kasar nan dangane da halin da ake ciki?
Solomon Dalung: To, na farko ina ba al’ummar Najeriya hakuri kan halin da mu shugabannin Najeriya muka sanya su. Domin mu shugabannin Najeriya ba mu rike musu amana ba, ba mu kare su yadda ya kamata ba. Kuma ba mu kyautata musu ba, a cikin ayyukanmu da halayenmu. Don haka dole su kara hakuri kuma su ci gaba da rokon Allah Ya kawo wa kasar nan zaman lafiya Ya tona asirin dukan wadanda suke cin gajiyar rigingimun da suke faruwa a Najeriya kuma Ya kawar da duk wanda ya zama ginshikin rigimar da take faruwa a Najeriya.