✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zargi jami’an Kwastam da kashe fasinjan mota a Shika

Ana zargin wadansu jami’an Kwastam da harbin wani magidanci kuma fasinjan wata mota inda ya rasa ransa, lokacin da suka biyo wata motar fasinja a…

Ana zargin wadansu jami’an Kwastam da harbin wani magidanci kuma fasinjan wata mota inda ya rasa ransa, lokacin da suka biyo wata motar fasinja a kan hanyar Shika, a Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadin makon jiya a kokarin jami’an na sanin abin da motar take dauke da shi, inda direban motar ya ki tsayawa, su kuma jami’an suka bude wa motar wuta da bindiga. Magidancin mai suna Sama’ila Dan Birnin Magaji a Jihar Zamfara da ke tare da ’ya’yansa biyu ya rasa ransa.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa motar fasinjan ta fito ne daga Jihar Zamfara zuwa Zariya, sai jami’an Kwastam suka yi kokarin tsayar da motar, amma direban bai tsaya ba, inda nan take jami’an suka bude wa motar wuta, suka samu daya daga cikin fasinjojin da motar ta dauko mai suna Sama’ila; wanda harbin ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take.

Majiyar ta kara da cewa, “Direban motar ya sauke gawar marigayin da ’ya’yansa biyu kanana, ya gudu ya bar su a wurin. Da gari ya waye sai aka ga yara kanana biyu a jikin gawar   mahaifinsu suna kuka sai aka duba aka ga yana da raunin harbin bindiga a jikinsa.

Kuma da aka sanar da Shugaban Karamar Hukumar Giwa cewar ga abin da ya faru sai shugaban ya ba da umarni cewa a dauki matakin ganin cewa an gano abin da ya faru da marigayin sannan a kula da yaran. Sai jami’an ’yan sanda na Giwa suka yi bincike, inda aka gano cewa jami’an Kwastam ne suka harbe marigayin. An yi amfani da wayar da aka samu a jikin gawar marigayin, aka kira ’yan uwansa aka sanar da su cewa ga abin da ya faru. ’Yan uwan marigayin sun taso daga Zamfara, suka zo kuma suka tabbatar da cewa dan uwansu ne Sama’ila kuma su mutanen garin Birnin Magajin Dan Ali na Jihar Zamfara ne. Marigayin ya taso daga Zamfara ne zuwa garin Abuja tare da ’ya’yansa biyu.

’Yan uwan marigayin sun roki cewa tunda Allah Ya yi masa cikawa, suna so a yi masa jana’iza a nan garin Giwa. Shugaban Karamar Hukumar Giwa Injiniya Abubakar Shehu Lawal Giwa ya dauki nauyi tare da ba da umarni cewa a yi masa jana’iza, tunda ’yan uwansa sun amince da haka.

Wani jami’in ’yan sanda da ya ce a sakaya sunansa ya ce sun nemi bayanai daga jami’an Kwastam da ke tsayawa a kan wannan hanya amma sun ce ba su ba ne suka aikata wannan kisa ba, amma abokan aikinsu ne, masu aiki na musamman suka yi aiki a ranar da abin ya faru. Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin jami’an hukumar Kwastam da ke sintiri a wannan hanya amma sun ki cewa uffan.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu A. Sabo ta hanyar buga masa wayar hannu har sau biyar, tare da tura masa sakon tes amma har zuwa hada wannan rahoton bai amsa ba.