✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi zanga-zanga kan rashin ruwa a Jihar Nasarawa

Mutane a Jihar Nasarawa sun gudanar da zanga-zangar lumana mafi girma a tarihin jihar kan rashin ruwan sha a kusan fadin jihar. Masu zanga-zangar da…

Mutane a Jihar Nasarawa sun gudanar da zanga-zangar lumana mafi girma a tarihin jihar kan rashin ruwan sha a kusan fadin jihar. Masu zanga-zangar da suka fito daga kananan hukumomin jihar 13 sun taru ne a ofishin Hukumar Ruwa ta jihar da ke hanyar Shendam a Lafiya ranar Juma’ar da ta gabata.

Da yake bayyana wa manema labarai makasudin zanga-zangar, Malam Musa Isma’il daga Lafiya ya ce al’ummar jihar daga dukkan kananan hukumomi 13 sun yanke shawarar turo da wakilansu zuwa Lafiya don gudanar da zanga-zangar ce saboda rashin ruwan sha da suke fuskanta kimanin wata shida da suka gabata duk da cewa suna biya kudin ruwan. Ya ce al’ummar jihar ba su taba fuskantar irin wannan lamarin ba, inda ya ce gwamnatin jihar da ta shude ta yi ta yi musu alkawari cewa za ta farfado da fannin ruwa a jihar amma har ta kammala wa’adinta ba ta yi komai ba. Ya ce maimakon haka sai aka yi ta fasa wasu bututun ruwa da aka binne a kasa lokacin da ake gyara da gina hanyoyi a garuruwan jihar musamman a Lafiya.

Ya ce, “Saboda haka muka taru a nan don bayyana wa sabuwar gwamnatin jihar a karkashin Injiniya Abdullahi Sule damuwarmu.”

Kokarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin daraktan hukumar  ruwan ya ci tura domin bai amsa wayarsa. Amma binciken wakilinmu ya gano hukumar ta daina tura ruwa ga jama’a a kusan dukkan sassan jihar a kimanin wata shida da suka gabata.