✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa matashi bulala 40 kan shan Mangwaro lokacin azumi a Jigawa

An yi wa wani matashi mai suna Ibrahim Isma’il, mai shekara 20, bulala 40, sakamakon shan mangwaro a bainar jama’a a lokacin Azumin watan Ramadan.…

An yi wa wani matashi mai suna Ibrahim Isma’il, mai shekara 20, bulala 40, sakamakon shan mangwaro a bainar jama’a a lokacin Azumin watan Ramadan. Wata kotun Shari’ar Musulunci ce dai ta samu matashin da laifin cin abinci a lokacin da musulmi ke azumtar watan Ramadan, a Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.

Alqalin kotun, Safiyanu Ya’u ya bayar da umurnin da a yi wa matashin bulala 40 a bainar jama’a cikin kasuwar garin, da nufin hakan ya zama izina ga jama’a. Alkalin ya ce, abin da Ibrahim ya aikata ya ci karo da sashe na 370 na dokokin hukunta laifuka na Jihar ta Jigawa.

Jami’an hukumar Hisba ne dai suka kame Ibrahim yayin da yake shan Mangwaron, a daidai lokacin da musulmin da suka mallaki hankali ke azumtar Ramadan.

An dai masa bulalar a tsakiyar Kasuwar Ringim, a gaban jama’a, yayin da aka bukaci taron jama’ar da su zama suna kirga bulalan da ake yiwa matashin.