Gwamnatin kasar Rwanda ta yi wa malaman firamare karin albashi da kashi 88, malaman sakandare kuma da kashi 44.
Gwamnati ta ce karin zai soma aiki ne daga wannan wata na Agusta.
- ‘Akwai ’yan majalisa da dama masu goyon bayan yunkurin tsige Buhari’
- An kama mutum 84 kan zargin yi wa mata 8 fyade a Afirka ta Kudu
Ta ce ta dauki matakin yi wa malaman karin albashi ne domin inganta rayuwarsu duba ga gudunmawar da sukan bayar ga cigaban kasa.
Firan Ministan kasar, Edouard Ngirente ne ya bayyana haka a ranar Litinin sa’ilin da yake yi wa majalisar kasar bayani kan halin da fannin ilimin kasar ke ciki.
Ngirente ya ce sabon tsarin albashin malaman ya nuna malaman firamare sun samu karin albashi da kashi 88 cikin 100, yayin da malaman sakandare suka samu karin kashi 40.
Jaridar New Times ta ruwaito cewa, kafin wannan lokaci malaman firamare sabbin dauka na karbar albashi na Rwf50,849 inda a yanzu za su rika karbar Rwf95,596 albarkacin karin da aka yi.