Babban Alkalin Jihar Ondo, Mai Shari’a Williams Akintoroye, ya yi afuwa ga fursunoni 18 da ke gidajen yari a Jihar Ondo.
Fursunonin da aka yi wa afuwa na zaman shari’a daban-daban kan manyan laifuka da suka hada da kisan kai da fyade da hada baki don aikta laifi da sauran fursunonin.
Sun samu afuwar ne a lokacin da Babban Alkalin ya kai ziyarar aiki ta farko a dukkanin cibiyoyin tsare mutane hudu da kuma cibiyar mata da ke Jihar Ondo tare da wasu Alkalai, inda ya umarci da su kasance masu halin kirki yayin da suka samu ’yanci.
Kwanturola na Hukumar, Mista Opeyemi Fatinikun wanda shi ne babban mai masaukin baki, ya yaba wa Babban Alkalin bisa namijin kokarin da ya yi na ganin ya ziyarci dukkanin cibiyoyin kula da ’yan sandan jihar duk da takaitacciyar sanarwar da aka bayar.
Shi kuma Babban Alkalin ya yaba wa Kwanturola da dukkan ma’aikatan bisa hadin kan da suke bayarwa wajen tabbatar da tsaron dukkanin cibiyoyin da ake tsare da fursunoni a jihar.
A cewar kakakin rundunar, Tunde Ogundare kuma ya nemi fursunonin su tafi kada su kara aikata laifi.