✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa basaraken gargajiya kisan gilla a Kurosriba

A makon jiya ne wasu ’yan ta’adda da ba a sani ba suka yi wa Cif Eyo Eyo Bassey, Dagacin kauyen Ikot-Obot da ke karamar…

A makon jiya ne wasu ’yan ta’adda da ba a sani ba suka yi wa Cif Eyo Eyo Bassey, Dagacin kauyen Ikot-Obot da ke karamar Hukumar Bakassi, Jihar Kurosriba kisan gilla.

Wannan al’amari ya afku ne a kauyen Ikot-Effiom, yankin Bakassi. Kisan basaraken kamar yadda wata majiya da ta bukaci a sakaya suna ta ce yana da nasaba da zarginsa da hannu a wani rikicin gona da ake zato ya taka rawa a lamarin. Ana zaton wadanda hukuncin bai yi wa dadi ba ne suka tura masa makasa, suka kashe shi.

Majiyar labarin ta ci gaba da cewa: “Rikici ne tsakanin wasu magada da shi sarkin da kuma sauran al’ummar gari. Maganar ma tana kotu, kafin a kai ga yanke hukunci wasu suka daukar wa kansu doka a hannu, suka kashe dagacin.”

Aminiya ta ci gaba da tattara bayanai daga wadanda suka zanta da ita kan kisan basaraken. An kuma shaida mata cewa: “Makasan sun fi su biyu kuma dirar mikiya suka yi wa gidan basaraken da ke Ikot-Obot, daura da makarantar firamare ta Effiom, suka kashe shi, suka kuma sulale ba tare da an kama ko daya daga cikinsu ba. Da suka shiga gidan, sai suka shiga sararsa da adduna har suka ci galabarsa; sai da suka ga ya mutu suka bar gidan.”

Aminiya ta tuntubi matar basaraken da aka kashe game da lamarin, wadda ta ce: “Ba ni da ta cewa kan wannan al’amari. Aika-aika dai an riga an yi ta.”

Wakilinmu ya ji ta bakin Irene Ugbo, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kurosriba game da lamarin, ta ce: “Tabbas mun samu labarin afkuwar kisan kuma muna nan muna ci gaba da yin bincike har sai an gano wadanda suka aikata hakan.”