An yi wa Babban Darektan Sashin Intanet da Harkokin Labarai na Rukunin Kamfanin Media Trust, Malam Naziru Mika’ilu Abubakar rashi a wannan Juma’ar.
Yayar Malam Naziru, Wasila Mika’ilu Abubakar ce dai ta rasu tana da shekaru 42 kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.
- Zan dinke barakar da ke tsakanin Gwamnati da Kiristocin Kaduna — Uba Sani
- Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza — Qatar
Malam Naziru ya tabbatar da rasuwar ’yar uwar tasa wadda yake bi, inda ya ce ta rasu cikin dare doshin Asubahin wannan Juma’ar.
An dai yi jana’izar marigayiya Wasila da misalin ƙarfe takwas na safiyar yau, kuma aka binne gawarta a makabartar Kofar Mazugal da ke kwaryar birnin Dabo.
Wasila wadda ta yi karatu a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano, ta rasu ta bar ’ya’ya biyar—maza uku da mace biyu.
Da yake zantawa da wakilinmu, dan uwar marigayiyar, Umar Mika’ilu na BBC, ya bayyana rasuwar Wasila a matsayin babban rashi kasancewar ta zama inuwar mahaifiya a gare su.
Umar ya ce “za mu yi kewarta kwarai saboda mace ce mai son zaman lafiya da kulawa wadda ta zama abar kauna a wurin duk wanda ya rabe ta.
“Ta yi rayuwarta a kan turbar neman ilimin addini da na zamani. Muna addu’ar Allah Ya jikanta Ya sa ta huta.”
Aminiya ta ruwaito cewa, a shekarun baya-bayan nan dai an yi wa Malam Naziru manyan rashe-rashe da suka haɗa har da na mahaifansa.
Ana iya tuna cewa, a watan Yulin 2021 ne mahaifiyarsa Hajiya Rakiya Muhammad ta rasu bayan shafe shekaru 67 a doron kasa.
Kazalika, a watan Mayun shekarar 2020 ce mahaifinsa, Malam Miko Alhassan ya riga mu gidan gaskiya bayan ’yar takaitacciyar jinya.