✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa Ajami kisan mummuke

Kafin Turawan mulkin mallaka su ci kasar Hausa da yaki, a shekarar 1903, rubutun Ajami shi ne tsarin dam asana ke amfani da shi a…

Kafin Turawan mulkin mallaka su ci kasar Hausa da yaki, a shekarar 1903, rubutun Ajami shi ne tsarin dam asana ke amfani da shi a harkar sadarwa, inda tsarin rubutun ya shahara a karkashin daular Fulani, har zuwa lokacin mujadaddin addini Shehu Usman danfodiyo, wato tsakanin shekarun 1754 zuwa 1817; ya kuma kafa daular Musulunci a tsakanin shekarun 1808 zuwa 1903.
Zamin mulkin mallaka, rubutun ajami ya hadu da cikas, inda aka bullo da dabarun dakile, ta hanyar bullo da rubutun boko, wajen juya haruffan Romawa a tsarin rubutun Hausa.
Turawan mulkin mallaka, sun yi ta bin hanyoyi daki-daki wajen shimfida mulkinsu a daukacin fadin kasar Hausa, amma duk da haka ba su samu nasarar kashe rubutun ajami ba. Kuma a tsarinsu sun yi dabarar mayar da Hausa ita kanta ta zama harshe na biyu da ake amfani da shi a hukumance, don haka tsarin Hausar boko ko rubutun gharuffan Latin da Romanci suka samu gindin zama.
Ba a taba gano illar da suka yi wa al’ummar wannan yanki ba, har sai da kasar ta samu ’yancin kai a shekarar 1960. Bayan sun mika mulki, sun tafi, sai wasu masana a wannan yankin suka yi ta kokarin farfado da rubutun ajami. Don haka sai da ta kai ga kimanin kasha 90 cikin 100 na mutanen da ke wannan yanki na Arewacin Najeriya sun fahimci wannan tsarin rubutu, kuma sun yi amfani da shi.
Wannan yunkuri da masana suka yi a kasar Hausa, ya samu karin tagomashi a Jamhuriya ta biyu, lokacin da Gwmanan farko na farar hula a Jihar Kano, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, ya bullo da jaridar da aka yi ta wallafata a cikin ajami, tsawon mulkinsa na shekarun 1979 zuwa 1983. Kuma daga bisani duk gwamnatocin da suka biyo bayansa sun kyale wannan jarida ta ci gaba da bunkasa.
Kafa jaridar ajami, mai lakabin Afijir ya haifar da wani juyin juya hali a siyasar Arewacin Najeriya, da wadansu yankunan na Afirka ta Yamma.
Masana a kasar Hausa da ke sassa-sassa daban-daban na kasar nan sun taimaka matuka gaya wajen yin rubuce-rubuce,. Kan al’amuran da suka shafi ra’ayi da siyasa da addini da zamantakewa da tattalin arziki, musamman harkokin kasuwanci a cikin wannan jarida, wadda ta wanzu a tsakanin shekarun 1980 zuwa 2012.
Jaridar Alfijir ta kara samun tagomashi a lokacin da ta dauki hankalin Hukumar Yada al’adu da Ilimin Kimiyya na Majalisar dinkin Duniya, wato “UNESCO,” inda aka rika gayyatar masu wallafa jaridar tarurrukan kara wa juna ilimi, musamman ma’aikatan Kamfanin dab’i na Triumph da ke gidan Sa’adu Zungur, a filin tsohuwar tashar kuka da ke birnin Kano. Editoci da masu aikin dabi’i, sun halarci tarurrukan duniya da aka sha gudanarwa a kasar Moroko.
Wannan shi ne dalilin da ya sanya marubuciyar wannan makala take yi wa al’umma tuni kan muhimmancin ajami, tare da nuna takaicinta kan yadda gwamnatin Jihar Kano ta dauki mummunan mataki wajen rufe madabba’ar da ke buga wannan jarida ta ajami. Alhali sanin kowa ne, cewa, wannan madabba’a ta yada ilimi a daukacin fadin Afirka ta Yamma. Kuma a siyasance, wadansu na ganin akwai gaba da aka nuna wa wadanda suka asassa jaridar Ajami da gwamnati mai ci yanzu ke yi. Sai dai sahihin al’amari da kowa zai iya amincewa da shi, shi ne, gwamnatin Jihar Kano ta tafka babban kuskure, domin ko da za ta kashe jaridun Turanci, tunda ko’ina ana yawan wallafe-wallafe da Ingilishi, sai ta yi kokarin ririta Ajami, ta yadda dimbin almajiran ilimi Muhammadiyya za su ci gajiyarsa tsawon zamani. Sannan da akwai hankali da tunani a cikin wannan al’amari, ai da an ci gaba da bunkasa ajami, musamman a wannan zamani da ake son ganin almajiran makarantun allo da na Islamiyya sun tafi bai daya da na zamani, wajen tsara manhajar karatu.
Uwa-uba dai, a iya cewa, kuskuren da gwamnati mai ci ta yi na kulle gidan Triumph wannan ra’ayin kanta ne, amma durkusar da rubutun ajami, illa ce ga mafi yawan al’ummar Kano da ma daukacin mutanen Afirka ta Yamma, wadanda har yanzu suke rubutu da ajami.
Tunda wannan gwamnatin tata ta kare, to duk wanda Allah Ya bai wa mulkin Jihar Kano a zabe mai karatowa, daga cikin hidimar da zai yi wa al’umma, akwai bukatar farfado da jaridar Ajami. Kuma su ma kamfanoni masu zaman kansu a harkar yada labarai, musamman Daily Trust da ke buga jaridar Aminiya su yi kokarin raya ‘Ajami,’ ta hanyar bude madabba’a kacokan don samar da litattafai da mujallu da jaridun ajami.
Matukar al’ummar wannan yanki, suka ci gaba da yi wa al’amarin ajami rikon sakainar kashe, babu shakka sai mu yanke cewa, an yi wa ajami kisan mummuke.
Na tabbata idan har aka raya rubutun ajami, za a ci gaba da amfani da shi wajen yada ilimi a fannoni da dama, kuma harkar aikin jarida zai kara samun tagomashi, har a tsakanin almajiran makarantun allo da na Islamiyya. Da zarar an samu wasu jajirtattun mutane wadanda suka yunkura wajen ilimantar da al’umma a cikin tsarin rubutun Ajami, to tattalin arziki da siyasa da addini da sauran fannonin rayuwa za su fadada a tsakanin al’ummar Afirka ya Yamma, musamman a Najeriya da Nijar.

Amina Abdullahi ta rubuto makalarta daga Unguwar Gandun Albasa cikin birnin Kano.