✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi jana’izar mai kulob din Leicester City

A ranar Litinin da ta gabata ne aka yi jana’izar mai kulob din Leicester City da ke Ingila Bichai Sribaddhanaprabha bayan ya mutu a wani…

A ranar Litinin da ta gabata ne aka yi jana’izar mai kulob din Leicester City da ke Ingila Bichai Sribaddhanaprabha bayan ya mutu a wani hadarin helicopter na lashin kansa jim kadan bayan an tashi wasa a tsakanin Leicester City da West Ham United a gasar firimiyar Ingila.

A wasan, an tashi ne 1-1 kuma marigayin yana daga cikin wadanda suka kalli wasan kai tsaye.

Rahoton da kafar watsa labarai ta The Mirror da ke Ingila ta ruwaito ta ce a yayin jana’izar akwai matarsa Aimon da babban dansa Aiyawatt da kuma ’yarsa Boramas.

Rahoton ya ce Allah ne ya kiyaye da hadarin ba zai rutsa da babban dansa Aiyawatt ba, don a lokacin mahaifin ya aike shi Thailand don gudanar da wadansu harkokin kasuwancinsa, kuma shi ne Mataimakin Shugaban kulob din Leicester City.

Marigayin wanda dan asalin Thailand ne, yana daga cikin attajiran da suka mallaki kulob a Ingila.

Tuni hukumar lwallon lafa ta Ingila ta aika salon ta’aziyya ga iyalan mamacin.

Marigayin ya rasu ne a hadarin tare da wasu mutum biyar, kuma rahotanni sun tabbatar babu wanda ya tsira daga cikinsu bayan jirgin ya fado sannan ya kama da wuta a kusa da filin wasan Leicester City.

Wilfred Ndidi, dan lwallon Super Eagles na daga cikin wadanda suke buga wa kulob din lwallo a Ingila.