✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi hatsarin jirgin sama a Legas

Wani jirgin sama ya yi karo da katangar filin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas, inda ya yi masa lahani. Hukumomin filin jirgin…

Wani jirgin sama ya yi karo da katangar filin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas, inda ya yi masa lahani.

Hukumomin filin jirgin ba su kai ga bayyana musabbabin hatsarin ba, sai dai wasu majiyoyi sun ce burkin jirgin ne ya samu matsala.

Jirgin mai lamba 5N-HIS ya daki katangar ne a lokacin da yake kokarin yin fakin a kusa da rumfar jiragen Bristow Helicopters.

Jami’in Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (NCAA) sun ziyarci wurin da abin ya faru domin gano irin barnar da aka samu.

Lamarin ya afku ne a safiyar Juma’a, da jirgin mallakin kamfanin Jet Air kirar King Air 200 wanda sashen jirage na kamfanin Mobil Oil Nigeria ke kula da shi.