Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wata Darakta a Kotun Shari’ah mai suna Hajiya Aishatu Muhammad Munjalo a gidanta da ke Doka Mai Jama’a yankin Kujama a Karamar Hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Masu garkuwan sun kuma harbe danta mai Suna Abdurrauf Muhammad bayan ya yi kokarin hana su tafiya da mahaifiyarsa.
Lamarin ya auku ne da misalin karfe 6:30 na safiya jiya Laraba a lokacin da suka yi wa gidan dirar mikiya.
Aminiya ta samu bayanin cewa, tuni aka yi wa mamacin sutura a yayin da kuma yan uwan ke jiran masu garkuwa da mutane su kira domin sanin halinda Hajiyar ke ciki.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce, tuni sun tuntubi sashen da yake da masu garkuwa da mutane domin su taimaka wajen gano mutane.