✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da Kwamishina a Binuwai

’Yan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan yada labarai na Jihar Binuwai a gidansa

Masu garkuwa da mutane sun sace Kwamishinan Yada Labarai, Al’adu da Yawon Bude Ido na Jihar Binuwai, Mathew Abo.

Wani ganau ya shaida wakilinmu ya ce da misalin karfe 8 na dare ne ’yan bindiga a kan babubra suka kutsa gidan Abo da ke mahaifarsa a yankin Zaki-Biam da ke Karamar Hukuamr Ukum ta jihar, suka yi awon gaba da shi.

Tsohon kakakin gwamnan jihar, Tahav Agerzua ya ce sai da ’yan bindigar suka tilasta daukacin mutanen gidan kwanciya a kasa, sannan suka dauke shi a kan babur zuwa inda ba a sani ba.

An yi garkuwa da Mathew Abo ne kasa da wata guda bayan an rantsar da shi a matsayin kwamishina a ranar 29 ga watan Agusta.

Karamar Hukumar Ukum na daga cikin wuraren da suka yi kaurin suna wajen ayyukan masu garkuwa da mutane a baya-bayan nan a jihar.