✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da basarake a Kaduna

Yanzu dai mutum 15 aka yi garkuwa da su a mako biyu duk a yankin

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dagacin Sabon Yelwa da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, Alhaji Safiyanu Muhammad da wasu mutum hudu.

Maharan sun kutsa gidan basaraken ne da tsakar daren Lahadi, suka dauke shi suka kuma hada da wasu maza uku da wata mata.

Dansa mai suna Yusuf Danbaba Safiyanu ya tabbatar wa wakilinmu cewa masu garkuwar sun kira su suna neman kudin fansa Naira miliyan 35.

Ya ce mutanen “sun so su yi garkuwa da wani mutum amma da ba su same shi ba sai suka daba wa mahaifin mutum wuka a hannu”.

Yusu ya ce sun sanar da ‘yan sanda game da lamarin kuma har sun je garin domin fara bincike.

Wakiliyarmu ta nemi karin bayani daga Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jagile, sai ya ce mata zai tuntube daga baya idan ya gama tattara bayanai.

Garkuwa da mutanen a Karamar Hukumar ta Igabi na zuwa ne mako biyu bayan ‘yan binidga sun sace wasu mutum 20 bayan sun kashe wasu mutum biyu a unguwar Dambushiya da ke Karamar Hukumar Chikun.

A karshen makon da ya gabata kuma masu garkuwa suka dauke wata jami’ar dan sanda da diyarta da wasu mutum hudu a unguwar Janruwa, a Chikun din mai makwabtaka da Igabi.