✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi bikin kaddamar da shugabannin Babbar Kasuwar Katsina

A ranar Asabar da ta gabata ne aka yi bikin kaddamar da shugabannin Babbar Kasuwar Katsina a babban ofishin gudanarwa na kasuwar. Gwamnan Jihar Katsina…

A ranar Asabar da ta gabata ne aka yi bikin kaddamar da shugabannin Babbar Kasuwar Katsina a babban ofishin gudanarwa na kasuwar.

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari wanda Shugaban karamar Hukumar Katsina kuma Shugaban kungiyar kananan Hukumomi (ALGON) na Jihar Katsina, Alhaji Lawal Lada ya wakilta, ya yi kira ga ‘yan kasuwar jihar da su yi kokarin rage farashin kayayyaki musamman kayan masarufi a cikin wannan wata mai alfarma na azumin Ramadan.
Ya ce ya zama wajibi ga ‘yan kasuwar bisa la’akari da cewa mafi yawan lokuta akan samu wasu ‘yan kasuwar da ke karawa farashin kayayyakin cikin wannan wata maimakon kawo sauki. Daga nan ya ce, gwamnatinsa a shirye take wajen tallafawa kungiyar da kuma ‘yan kasuwar domin habaka harkokin kasuwanci a duk fadin jihar.
Tun farko sai da babban bako a wajen taron Mai Shari’a Musa danladi Abubakar ya yaba wa kungiyar a wajen kokarin da take yi wajen ilmantar da ‘ya’yanta akan yadda za su ci gaba da tafiyar da harkar kasuwanci a zamanance. Har ila yau, ya ce akwai bukatar kara fadakar da su sanin muhimmanci da wajibcin sanin tanade-tanaden shari’ar Musulunci akan harkokin saye da sayarwa. Ya kara da cewa, “kadan daga cikin abubuwan da ‘yan kasuwar za su lura da su sun hada da sanin abin da za ayi kasuwancin da shi, sanin bambanci a tsakanin riba da ribaa, kyautatawa a wajen mu’amulla, kiyaye murdiya da ha’inci tare da yin huldar kasuwanci ta zamani musamman ta hanayar Intanet wadda ta dace da shari’a.”
Mai Shari’an ya shawarci mambobin kungiya da su “zamo masu biyayya ne ga wadannan shugabanni, su kuma shugabannin su zamo masu adalci ga wadanda suke shugabanta.”
A na shi bangaren Shugaban kungiyar ‘yan Kasuwar Jihar Katsina, Alhaji Musbahu Mai Zare, ya bayyana farin cikinsa akan yadda aka samu nasarar yin zaben shugabanni, kimanin wata daya da ya wuce, wanda yake shi ne na farko a tarihin kungiyar. Ya ce, “uwar kungiya ta jiha ta yi iyakar duk abin da za ta yi na ganin an samu nasarar zaben, inda kwalliya ta biya kudin sabulu.” Daga nan ya yi kira ga shugabannin da kuma sauran ‘yan kasuwar da su jajirce su kuma bi duk wata hanyar da ta kamata don ganin cewa sun inganta kungiyar tare da ciyar da harkokin kasuwanci gaba.
Da yake nashi jawabin bayan kaddamar da su, sabon zababben shugaban kungiyar Alhaji Abbas Labaran Albaba ya ce,za su ba marada kunya ta hanyar shugabancin wannan kungiyar bisa adalci da rikon amana. “A shirye muke na ganin cewa, mun bi dokoki da ka’idojin da kungiya ta kafa. Kuma za mu yi iya kokarinmu na ganin cewa mun bi hakkin kungiya da na ’ya’yanta a duk inda suke don tabbatar da shi ga mai shi. Hakazalika, za mu kara bunkasa harkokin kasuwanci a wannan jiha.”
An dai zabi shugabanni 19 da suka hada da Alhaji Abbas Labaran Albaba a matsayin shugaba. Sai Alhaji Murtala Abubakar Mainasibi a matsayin mataimakinsa da Bello Sama’ila Sakatare da Muntari Bawa a matsayin Ma’aji da Rabi’u Muhammad Sarki Mai bincike tare da Ibrahim Alka a matsayin Jami’in hulda da jama’a. Har ila yau, akwai Hajiya A’isha Kabir Idris a matsayin Jagorar matan kungiyar.
An kafa wannan kungiyar ne a shekarar 1971 a lokacin da ake cikin tsohuwar kasuwa ta cikin garin Katsina,wadda Alhaji Amadu Gege ya jagorance a matsayin shugaba na riko. karkashin jagorancin Gege ne aka dawo wannan kasuwa wadda Gwamnan mulkin soja Kanar Akagege na wancan lokaci ya gina a cikin shekarar 1997. An gina manyan shaguna da kananan sama da dubu biyu. Daga bisani wannan kungiya ta sake samun Musbahu Maizare a matsayin wani shugaban rikon kungiya wanda a karkashinsa ne aka yi zaben shugabanni kungiyar na farko a bana.