✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi arangama tsakanin direbobin tasi da jami’an tsaftace Abuja

Direbobin tasi sun gudanar da zanga-zanga nuna kin jinin kwamitin hadin gwiwa na tsaftace garin Abuja. Direbin da suka harzuka sun rika kona tayoyi tare…

Direbobin tasi sun gudanar da zanga-zanga nuna kin jinin kwamitin hadin gwiwa na tsaftace garin Abuja.
Direbin da suka harzuka sun rika kona tayoyi tare da hana zirga-zirga a manyan hanyoyin birnin da titin babbar kasuwar Abuja inda suka rika nuna fushinsu ga yadda jami’an kwamitin tsaftace Abuja kan cin zarafin membobinsu.
Aminiya ta gano cewa jami’an tsaron sun yi wa direbobi uku duka sannan suka jefa su cikin motarsu suka kai su ofishin ’yan sanda da ke unguwar Garki a Abuja.