✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…An yanke wa wani hukuncin kisa

A wata shari’ar, Mai shari’a Ahmed Abubakar Kazaure ya yanke wa wani tsoho mai suna Mohammad Sabitu Bashir mai shekara 57 da ke garin Bula…

A wata shari’ar, Mai shari’a Ahmed Abubakar Kazaure ya yanke wa wani tsoho mai suna Mohammad Sabitu Bashir mai shekara 57 da ke garin Bula a Karamar Hukumar Taura ta Jihar Jigawa hukuncin kisa ta hanyar rataya

An yanke masa hukuncin ne saboda samunsa da laifin kashe wata mata ta hanyar sassara ta.

Daraktan Mulki da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Malam Auwalu Sani Balago ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce matar ta fito daga garin ’Yangayami a Karamar Hukumar Taura, a kan hanyarta ta zuwa kauyan Bula, sai mai laifin wanda ake zargi lokacin yana shaye-shaye ne ya tare ta ya daddatsa ta da magirbi har sai da ta mutu.