✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa mutum 4 hukuncin kisa kan kan garkuwa da Basarake

Alkalin Babbar kotun jihar Legas, da ke Ikeja Oluwatoyin Taiwo, ya bada umarnin hukuncin kisa ga mutum hudu da suka yi garkuwa Sarkin Iba, Oba…

Alkalin Babbar kotun jihar Legas, da ke Ikeja Oluwatoyin Taiwo, ya bada umarnin hukuncin kisa ga mutum hudu da suka yi garkuwa Sarkin Iba, Oba Goriola Oseni. Za yanke masu hukuncin ne ta hanyar ratayewa.

Wadanda za a yi wa hukuncin sun hada da: Duba Furejo, Ododomo Isaiah, Reuben Anthony, da Yerin Fresh. Kotun ta fara gurfanar da wadanda ake zargin ne tun a ranar 24 ga Oktoba 2016. Kamar yadda Daraktan Hulda da jama’a na Kotun ya sanar, ya kuma ce kotun ta samu wadanda aka yanke wa hukuncin da laifuka takwas cikin su akwai: kisan kai, fashi da makami, yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.