daya daga cikin ’ya’yan shahararren dan kwallon duniya Pele, mai suna Edinho an yanke masa hukuncin daurin shekara 30 a gidan kaso bayan an same shi da laifin yin facaka da dukiyar da ya samu ta hanyar yin hulda da kwayoyi.
Edson Cholbi Naseimento da aka fi sani da Edinho kotu ta same shi da laifin samun makudan kudi ta hanyar yin mu’amala da kwayoyi kuma ana kyautata zaton ya hada kai ne da shahararren mai safarar miyagun kwayoyi a kasar Brazil da aka kira Ronaldo (Naldinho).
Sai dai dan kimanin shekara 33 Edinno ya musanta cewa ya hada kai da kungiyar da ke safarar miyagun kwayoyin amma kuma ya tabbatar yakan sayi kwayoyin da yake safararsu daga wajen kungiyar daga lokaci zuwa lokaci.
Idan za a tuna, a shekarar 2004 mahaifinsa Pele ya barke da kuka jim kadan bayan jami’an tsaro sun bayar da sanarwar kama Edinho a harkar safarar miyagun kwayoyi.
A shekarar 1990 ne dan ya yi kokarin ya bi sahun mahaifinsa Pele a fagen kwallon kafa inda ya yi wa kulob din Santos kwallo na wani dan lokaci amma ba a dade ba ya bar su. Kulob din Santos ne Pele ya yi wa wasa a lokacin da yake ganiyar buga kwallo.
Haka kuma kotun Preia Grande da ke yankin Sao Paulo ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin daurin shekara 33 da su ma aka samu da laifin yin hulda da miyagun kwayoyi.
Pele da cikakken sunansa shi ne Arantes do Nascimento dan kimanin shekara 73 yana da ’ya’ya bakwai. Ya zama dan kwallon da har yanzu babu kamarsa a tarihin kwallon kafa a fadin duniya. Ya taimakawa Brazil wajen lashe kofin duniya sau uku kafin ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa.
An yanke wa Edinho dan Pele hukuncin daurin shekara 30
daya daga cikin ’ya’yan shahararren dan kwallon duniya Pele, mai suna Edinho an yanke masa hukuncin daurin shekara 30 a gidan kaso bayan an same…