✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tube kwamishina a Kano don murnar rasuwar Abba Kyari

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tube kwamishinansa na ayyuka, Injiniya Mu’azu Magaji, nan take bayan kwamishinan ya wallafa wasu kalama da suka nuna…

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tube kwamishinansa na ayyuka, Injiniya Mu’azu Magaji, nan take bayan kwamishinan ya wallafa wasu kalama da suka nuna yana murnar mutuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari.

Wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai Mohammed Garba ya fitar ta ce laifi ne irin kalaman da kwamishinan ya wallafa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati, “ya kamata ya kare martabar ofishinsa”.

“Gwamnatin Ganduje ba za ta lamunci irin wadannan kalaman daga wani jam’in jihar ba”, inji sanarwar.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Injiniya Muazu ya bayyana cewa “Win win (ma’ana, ‘yan kallo lafiya, mai wasa lafiya). Najeriya ta tsira, Abba Kyari ya mutu a cikin annoba.”

Kalaman da Kwamishinan ya wallafa sun janyo masa kakkausar suka daga mabiyansa a shafin Facebook, inda wasu suka yi masa martani suna cewa bai kamata mai mukamin kwamishina ya rika wallafa kalamai irin wadannan ba.