Masu garkuwa da jagoran Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a Kudancin Kaduna, Very Rabaran Jihan Mark Chietnum, sun hallaka shi.
Sanarwar da Cocin Rabaran Emmanuel Uchechukwu Okolo da ke Kafancan ta fitar, ta ce an gano gawarsa ce a ranar Talata.
- Rasha za ta ci gaba da katse wa kasashen Turai iskar gas —Putin
- Mutum 189 sun kamu da Kwalara a kananan hukumomi 20 a Kano
An yi garkuwa da limanin Katolikan kuma Shugaban CAN a Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna ne tare da wani limamin coci, Rabaran Donatus Cleopas.
A ranar 15 ga watan Yuli aka yi awon gaba da su a kauyen Yadin Garu na Karamar Hukumar Leren jihar, amma daga bisani Rabaran Donatus ya samu kubutowa daga hannun ’yan bindigar.
’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a Birnin-Gwari
Rahotanni daga yankin Karamar Birnin-Gwari na jiha sun ce ’yan bindiga sun hallaka mutum biyar a kauyen Ganin-Gari da ke yankin Randagi a Arewacin karamar hukumar.
Shugaban Kungiyar Masarautar Birnin Gwari, Ishaq Usman Kafai, ya ce mahara kusan 40 ne suka kai farmakin a kan babura a ranar Lahadi.
Ya ce sun kashe mutane biyu tare da kora shanu da kuma garkuwa da mutanen da ba a san adadinsu ba a kauyen.
Kafai dai ya ce rundunar tsaron hadin guiwar ’yan sa-kai da ke kusa da gadar Tudun Wada sun kwato dukkanin wadanda aka sacen da kuma shanun da suka kora.
“A hanyarsu ta komawa maboyarsu sun kashe wani yaro da suka ci karo da shi a kan titi a kusa da kauyen Dawakin Bassa.
“Sannan a ranar Litinin sun kashe wasu mutane biyu a gona, wanda jimilla ya zama mutane biyar ke nan”, in ji shi.