Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta ce ta tsinci wani jariri da ake zargin mahaifiyarsa ce ta jefar da shi a cikin wani kwandon shara.
Mai Magana da Yawun rundunar a jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce an tsinci jaririn ne kunshe cikin wata leda.
- Kamfanonin waya za su yanke hulda da bankuna saboda taurin bashi
- An fara bincike kan mutuwar yaro bayan an yi masa allura a Legas
Sai dai jami’in bai yi wani karin haske ba game da daidai inda aka tsinci jaririn.
An ga Hundeyin ya dora hoton jaririn a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, inda ya ce ba domin gano jaririn da aka yi a kan kari ba, da tuni ya mutu.
Ya kara da cewa a halin da ake ciki, jaririn yana cikin koshin lafiya.
Daga nan ya yi kira ga mata da su guji dabi’ar zubar da ciki, maimakon haka barin cikin shi ya fi zama alheri.
Ya ce jefar da jarirai babban laifi ne wanda ke tattare da hukunci mai tsanani.