✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar manomi bayan biyan N1.65m a matsayin kudin fansarsa

An tsinci gawar wani manomi da aka sace a Ibadan babban birnin jihar Oyo, makonni biyu da sace shi

An tsinci gawar wani manomi bayan mako biyu da sace shi duk da biyan Naira miliyan daya da dubu 600 da iyalansa suka yi a matsayin kudin fansa.

Mutumin mai suna Oluwole Agboola dai an sace shi ne tun ranar 28 ga watan Disambar 2020, kafin ranar Talata kuma a tsinci gawarsa.

Wasu ’yan bindiga sanye da kakin sojoji ne suka yi awon gaba da shi yana tsaka da aiki a gonarsa da ke kauyen Olukitibi na Karamar Hukumar Akinyele ta Jihar Oyo.

Rahotanni sun ce maharan sun kashe shi ne duk kuwa da karbar makudan kudaden daga hannun iyalansa a matsayin kudin fansa.

Wani dan uwan mamacin, Olakunle Agboola ya tabbatar wa da ’yan jarida cewa an tsinci gawar manomin ne a Ibadan, babban birnin Jihar.

Ya ce an kashe dan uwan nasa ne kwanaki 10 bayan karbar kudin fansarsa daga hannunsu.