✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsige shugaban Majalisar Ogun

Elemide Oludaisi mai wakiltar mazabar Odeda ya zama sabon shugaban majalisar.

Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta tsige shugabanta, Olakunle Oluomo.

A safiyar Talata mutum 18 daga cikin mambobin 26 da ke majalisar suka kada kuri’ar amincewa da tsige Oluomo mai wakilatar mazabar Ifo.

Kafin tsige Oluomo dai ana zargin sa da karkatar da kudaden majalisar Naira biliyan 2.5.

Bayan tsige shi mambobin majalisar suka zabi Honorabul Elemide Oludaisi mai wakiltar mazabar Odeda a matsayin sabon shugaban majalisar.

Sabon shugaban majalisar, Elemide, ya mai goyon bayan tsohon gwamnan jihar Olusegun Osoba ne.
A baya ya janye daga takarar shugabancin majalisar ne domin ba wa Oluomo damar samun tazarce.