An tsauraran matakan tsaro a cikin birnin Kano da kewaye yayin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya isa jihar domin kaddamar da ayyukan raya kasa guda takwas a jihar.
Buhari, ya isa Kano da misalin karfe 10:07 na safe, inda tuni ya kaddamar da aikin Tashar Jiragen Ruwa ta Tsandauri da ke Dala da kuma kamfani mai amfani da hasken rana a Zawachiki, kafin daga bisani ya isa Fadar Sarkin Kano.
- Zazzabin Lassa ya kashe mutum 13, ya kama wasu 115 a Edo
- Bayan kwan-gaba-kwan-baya, Buhari zai kaddamar da aiki 8 a Kano
Aminiya ta gano cewa tun da yammacin ranar Lahadi aka girke jami’an tsaro da suka hada da ’yan sanda da na Sibil Difens da jami’an hukumar kiyaye hadura da kuma hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar (KAROTA) a wasu hanyoyi don tabbatar da tsaro yayin ziyarar shugaba Buhari.
Hanyoyin da aka girke jami’an tsaron sun hadar da titin Sabo Bakin Zuwo, titin gidan Sarkin Kano, titin Ahmadu Bello da kuma titin Audu Bako.
Buhari zai kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawat 10 na gwamnatin tarayya da tashar jirgin ruwa ta Dala a unguwar Zawachiki da ke Karamar Hukumar Kumbotso.
Kazalika, zai kaddamar da cibiyar bayanai ta Jihar Kano da ke sakatariyar Audu Bako.
Sauran su ne Cibiyar Kula da Ciwon Daji da ke Asibitin Kwararru na Muhammadu Buhari a Giginyu, Rukunin Gidajen Gwamnatin Tarayya a Gandun Sarki da ke Darmanawa da sauran ayyuka.