Yayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke hanyarsa ta zuwa Jihar Legas domin ziyarar aiki, an jibge jami’an tsaro a filin jirgi sama na Murtala Muhammad don tarbarsa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa shugaban zai isa jihar ne ranar Litinin, domin kaddamar da wasu ayyuka.
- An dauke wutar lantarki a duk fadin kasar Pakistan
- NDLEA ta kama makaho da kuturu dauke da Tabar Wiwi
Jami’an tsaron da aka jibge sun hada da sojojin ruwa da na kasa da na farin kaya da na sama da sauransu, duk a sashin saukar Shugaban Kasa na filin jirgin..
Ayyukan da Buharin zai kaddamar sun hada da aikin tashar jiragen ruwa ta Lekki, da na hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da ta jihar da kuma wani kamfani mai zaman kansa mai suna Tolaram.
Kazalika a na sa ran zai kaddamar da kamfanin sarrafa shinkafa na ton 32 a kowace sa’a, wanda alkaluma suka bayyana cewa daya ne daga mafi girma a duniya.
Haka kuma akwai aikin cibiyar adana tarihi da al’adun al’ummar Yarabawa ta John Randle.