Jami’an tsaron kasar Masar sun tsare dan jaridar nan, Tukur Mamu, wanda ke shiga tsakani a sako fasinjan jirgin Abuja-Kaduna da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Tukur Mamu wanda ke hanyarsa ta zuwa Umrah a kasar Saudiyya ya ce jami’an tsaron Masar sun tsare shi tare da iyalansa ne bisa umarnin gwamnatin Najeriya, a birnin Alkahira na kasar Masar.
- Kamfanin Media Trust Zai Karamma Ma’aikatansa Da Suka Nuna Bajinta
- ASUU ta yi watsi da tayin karin albashin malaman jami’a
Ya ce bayan tsare su na tsawon yini guda hukumomin kasar Masar suka taso keyarsu zuwa Najeriya.
Tukur Mamu ya yi fice wajen shiga tsakani da taimakawa wajen ganin an sako fasinjojojin da ’yan bindiga suka sace a hanyar Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris, 2022.”
Wasu dai suna zargin dan jaridar kuma mawallafin jaridar Desert Herald da nuna alamar goyon bayan ’yan bindigar, zargin da ya musanta da kakkausar murya.
Ya shai wa Aminiya a hayar dawo da shi Najeriya cewa ranar Talata aka tsare shi a birnin Alkahira na kasar Masar, amma ba a same da shi da wani abu na laifi ba.
A cewarsa, hukuomin kasar Masar sun bayyana mishi cewa hukumomin Najeriya ne suka ba da umarnin tsare shi, amma bayan binciken da suka gudanar a kansa, babu dalilin ci gaba da rike shi a kasarsu.
Ya yi zargin cewa gwamnati na so ta tsare shi ne kamar yadda ta yi wa Sunday Igboho, wanda ke neman ballewa daga Najeriya domin kafar kasar Oduduwa ta Yarabawa zalla.
Amma a cewarsa, hukumoin Masar sun shaida masa cewa tunda yana da cikakkun takardun tafiya, bai kamata su ci gaba da tsare shi ba.