✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tallafa wa manoman rani a Jigawa da aikin N10bn

An bullo da shirin ne don taimaka wa manoman yankunan karkara.

Gwamnatin Tarayya a ranar Asabar ta damka wa kananan manoman rani a Karamar Hukumar Auyo ta Jihar Jigawa wasu ayyuka da darajarsu ta kai kimanin Naira biliyan 10.

Shirin, wanda ya kunshi kadada 2,000 na gonaki wanda yake samun tallafin Bankin Duniya an bullo da shi ne da nufin taimaka wa manoman yankunan karkara su ci gaba da noma tsawon shekara ba kakkautawa.

Hukumar Bunkasa Kogunan Hadeja da Jama’are (HJRBDA) ce dai take kula da shirin.

Da yake mika aikin ga Gwamna Badaru Abubakar na Jihar a kauyen Yamdi, Ministan Ruwa, Injiniya Sulaiman Adamu ya bayyana kammala aikin a matsayin cika alkawarin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dauka yayin wata ziyara a 2018.

A cewar Ministan, akalla kananan manoma 200 ne ake sa ran za su amfana da shirin.

Ya ce a tashin farko, aikin ya lashe Naira biliyan 9.3 ne, sai daga bisani aka kara Naira biliyan 1.48.

Minista Sulaiman ya ce ya zuwa yanzu aikin ya kai matsayin kaso 74 cikin 100 na kammalawa, inda ake sa ran nan da watan Yunin badi za a kammala shi baki daya.