✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tabbatar da mutuwar mutum 22 a hatsarin jirgi a kasar Nepal

Ma’aikata uku da fasinjoji 29 ne jirgin ke dauke da su a lokacin da ya yi hatsarin

Hukumomi a kasar Nepal sun ce duka mutum 22 da hatsarin jirgin sama ya ritsa da su a kasar a ranar 29 ga Mayu, 2022 sun rasu.

Gwamnatin kasar ta bayyana hakan ne a ranar Talata bayan da masu aikin ceto suka gano gawar karshe a inda jirgin ya yi hatsari.

Kakakin Hukumar Sufurin Jiragen Sama na Nepal, Deo Chandra Lal Karn ya ce, jira suke a samu yanayi mai kyau don su kwashi sauran gawarwakin da aka gano zuwa Kathmandu, babban birnin kasar.

Jami’in ya kara da cewa da jirgin sama mai saukar ungulu suka yi amfani wajen jigilar gawargwakin da suka gano zuwa Kathmandu a yammacin ranar Litinin.

Kazalika, ya ce za su mika gawarwakin ga ’yan uwan mamatan da zarar an kammala tantance su.

Jirgin saman ya yi hatsari ne kusa da Sanosware a Mustang da ke gundumar Himalayan, Arewa maso Yammacin Kathmandu, inda da farko aka sanar da bacewarsa.

Bayanai sun ce ma’aikata uku da fasinjoji 29 ne jirgin ke dauke da su a lokacin da ya yi hatsarin.

Jaridar Nepali Times ta ce daga 1997 zuwa 2022 an samu aukuwar hatsarin jirgin sama sau biyar a kasar, inda mutum 74 suka rasa rayukansu.

Hukumomin kasar sun ce an kafa kwamitin da zai gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin.