Gwamnatin Kano ta soke hawan Sallah da dukkan wasu bukukuwa da aka shirya gudanarwa a Jihar yayin bikin Babbar Sallar bana.
Matakin na zuwa ne kusan mako daya bayan Kwamitin Shugaban Kasa Kan Yaki da COVID-19 ya yi gargadin cewa jihohi shida, ciki har da Kano na cikin barazanar annobar da ta sake barkewarta a karo na uku.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Muhammad Garba, a cikin wata sanarwa ranar Litinin ya ce sai dai za a gudanar da Sallar Idi kamar yadda aka saba a dukkan masallatan da ke fadin jihar.
Ya ce daukar matakin na daya daga cikin hobbasar da Najeriya ke yi kamar sauran takwarorinta na Afirka wajen dakile sabon nau’in cutar da ake kira da Delta mai saurin yaduwa.
Garba ya ce hakan ne ya sa hukumomi a jJihohin da aka yi wa gargadin suka yanke shawarar takaita cunkoson jama’a, musamman yayin hawan sallah.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’umma ka su ci gaba da kiyaye matakan kariya daga cutar kamar sanya takunkumi da wanke hannuwa a-kai-a-kai da kuma bayar da tazara a lokacin Sallar Idin.