✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An shirya wa ‘yan-kato-da-gora 500 bita a Jigawa

Kungiyar Sintiri ta Jihar Jigawa da aka fi sani da kato-da-gora ta bai wa ‘ya’yanta su 500 horo a kan sanin makamar aiki a farkon…

Kungiyar Sintiri ta Jihar Jigawa da aka fi sani da kato-da-gora ta bai wa ‘ya’yanta su 500 horo a kan sanin makamar aiki a farkon wannan makon a Dutse.

Kwamandan kungiyar, Malam Usman Kazaure shi ne ya fadi haka a wata ganawa da ya yi da wakilimmu yana mai cewa mutum 500 ne suka amfana daga bitar, wadda manyan jami’an ‘yan sanda da cibil difens da DSS suka gabatar da kasidu ga mahalarta taron, domin koyar da su hanyoyin bunkasa aikinsu na tsaro.

“Makasudin bitar ita ce don a koya wa yaransa yadda zasu rika tattara bayanai na sirri da kuma yadda zasu rika aiwatar da aikinsu na tsaro ba tare da an sami wata matsala ba. “Mun shirya bitar ne ga daukacin wakilanmu na kananan hukumomin jahar 27 domin ya zama kowa ya amfana daga irin ilimin tsaron da muke bukata ace ‘yan sintirin sun samu,” inji shi

Yayin bitar, an raba wa ‘ya’yan kungiyar takardun shaidar halartar bitar, domin kara masu kwarin gwiwa a kan aikinsu. Sannan aka hore su da yin amfani da abin da suka koya a yayin bitar don tabbatar da sun aiwatar a aikace don amfani al’umma.