✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An shawarci Musulmi su gyara halayyarsu

Babban Limamin Masallacin Babban Masallacin birnin Benin, Imam AbdulFattai Inabulole ya yi kira tare da shawartar Musulmi da su gyara halayyarsu na ayyukan ibada da…

Babban Limamin Masallacin Babban Masallacin birnin Benin, Imam AbdulFattai Inabulole ya yi kira tare da shawartar Musulmi da su gyara halayyarsu na ayyukan ibada da na mu’amala; a cikin wata zantawa da Aminiya a garin Benin fadar mulkin Gwamnatin Jihar Edo.
Limamin kuma ya ce wajibi ne ga Musulmi suna tsare dokokin Ubangiji, suna bin umarninSa kamar yadda ya zo a cikin koyarwar Alkur’ani mai girma da hadisan manzon Alla (S.A.W). Sannan kuma ya ce ya kamata gaba dayan Musulmi su gane cewa babu abin da ya fi zaman lafiya muhimmanci.
“A Musulunci, babu nuna bambanci, don haka har kullum wannan addinin yana kirane a kan kadaita Ubangiji tare da zaman lafiya. Saboda haka Musulunci addini ne na hadin kai da kaunar juna da tausaya wa bayin Allah, marayu da matalauta da musakai da mata da yara kanana.” Inji Imam din.
Limamin ya jawo hankalin ’yan uwansa malamai masu tafsiri a masallatai da sauran wurare a lokacin azumi da su yi taka-tsan-tsan da fassara ayoyin Allah da ra’ayi ko batanci da kushe wa juna. Maimakon hakan ya ce su yi kokarin nuna wa mabiyyansu hanyar da za a samu zaman lafiya.