✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sanya min 40

An sanya min 40 Wani Bafulatani ne ya zo zai yi masa katin zama dan kasa, sai ya ce da shi da mahaifiyarsa ne amma tana…

An sanya min 40
 
Wani Bafulatani ne ya zo zai yi masa katin zama dan kasa, sai ya ce da shi da mahaifiyarsa ne amma tana gida. Aka tambaye shi cewa: “Shekarunka nawa?” Sai ya ce: “A sanya mini shekara 40. Ita kuma tunda mace ce, a sanya mata shekara 25.”
Daga mai lamba, 08039670323

Bagobiri

Wani Bagobiri ne yana tafiya tare da matarsa sai ya mutu, aka zo ana tambayar matarsa cewa ko yana Sallah? Ta ce: “Eh, mun yi Sallah babba a Shinkafi.” Aka ce mata a’a, ba wannan ba. Ta ce: “Oh, ko irin kankanan ga masu bata ruwa? In dai su ne bai yin su.”
Daga Alkasim Saddik, 07035863334

Motar haya

Wani saurayi ne ya kira budurwarsa, ya ce: “Dalin, kina ina ne?” Sai ta ce: “Wallahi ina cikin motar babana, zai kai ni makaranta.” Shi kuma sai ya ce mata: “To kada ki damu, domin ga ni nan zaune a gaban motar, har ma na biya miki kudin mota.”
Daga Babangida Ahmad Jibrin Gwarzo, 08141667702

Malam da ni yake yi

Wasu Yarabawa biyu ne abokan juna kuma dukkansu Musulmi, wata rana suka zo ci-rani Arewa sai dayansu ya shiga sayar da giya. Wata rana sai suka je jin wa’azi, suka samu malami yana wa’azi a kan giya, sai dayan ya tambaya cewa: “Mene ne hukuncin Musulmi mai sayar da giya?” Jin haka sai abokin nan nasa ya amsa da cewa: “Malam da ni yake yi, ci gaba da wa’azinki; in an tashi wa’azi zan ba shi amsa.”
Daga Laminu Umar Abba, 08131364647