✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu tsaiko a shari’ar Sarautar Kano

Babbar Kotun Jihar Kano ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 24 ga watan Yuni, 2024.

Rashin sadar da sammaci ga wadanda ake kara ya hana sauraron shari’ar rikicin Masarautar Kano da ke gaban babbar kotun jihar Kano a ranar Talata.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano bai samu damar sadar da sammaci ga Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan na masarautun jihar hudun da aka rushe ba.

Masu karar da suka hada da Kwamishinan Shari’a da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar da majalisar jihar sun shigar da karar ne ta hannun lauyansu Ibrahim Isah-Wangida.

Masu karar sun nemi kotu ta hana Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan hudu da suka hada da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da Sarkin Karaye, Dokta Ibrahim Abubakar ll, da Sarkin Rano Muhammad-Inuwa, da Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim-Gaya, bayyana kansu a matsayin sarakunan wadancan masarautu da aka rushe.

Sauran wadanda ake kara sun hada da Shugaban ’Yan Sandan Najeriya da Daraktan hukumar DSS da Kwamandan Hukumar Sibil defens da Rundunar Sojin Kasa.

Yayin zanan kotun na yau Lauyan Shugaban ’Yan sanda, Abdussalam Saleh ya shaida wa kotun cewa duk kokarinsu na sadar da sammaci ga wadanda ake kara abin ya ci tura.

Lauyan wadanda ake kara Eyitayo Fatogun SAN, ya nemi kotun ta sa wata rana don su sami damar hada duk wasu bayanai na sammaci ga wadanda ake kara.

Alkalin kotun, Mai sharia Amina Adamu Aliyu ta ce ‘ba daidai ba ne wanda ake kara na shida ya ki bayar da sammaci ga wadanda ake kara ba don wai akwai wani umarnin kotu da ya hana a kama ko cin zarafin sarakunan biyar ba.

“Abin da sharia ta sani shi ne kai za ka ba su sammaci ne kawai, don haka umarnin kotun farko ba zai dakatar da kai daga aikinka ba.

“Ya za a yi ka ba wanda ake kara na farko kariya sannan ka ce ka kasa sadar da sammaci gare shi?”

Mai Shari’a Amina Adamu ta dage shariar zuwa ranar 24 ga watan Yuni, 2024.

A ranar 27 ga Mayu kotun ta bayar da umarni ga wadanda ake kara ko ’ya’yansu ko bayinsu su daina ayyana kansu a matsayin sarakunan masarautun don samun dorewar zanan lafiya a Jihar Kano.

Haka kuma kotun ta umarci ofishin Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Kano da ya sadar da sammaci ga wadanda ake kara.

Aminiya ta rawaito cewa a ranar 23 ga Mayu Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sauke dukkanin sabbin masauratun Jihar guda hudu inda shi kuma gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sake nada Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.