An samu nasarar kwashe mahajjatan Najeriya dubu 71 zuwa Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin bana, duk da wasu ’yan kalubale da suka taso.
Shugaban Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) Barista Abdullahi Mukhtar Muhammad ne ya bayyana haka a Makka, lokacin da yake bayani ga masu ruwa-da-tsaki kafin mahajjatan sun tashi zuwa Mina da Arfa domin gudanar da aikin Hajji. Ya ce kimanin mahajjata dubu 65 ne suka je aikin Hajjin ta hannun hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, yayin da mahajjata dubu 16 da 200 suka je ta hannun kamfanoni masu zaman kansu.
Shi kuwa shugaban sashin sanya ido da tabbatar da bin ka’ida na Hukumar NAHCON, Alhaji Usman Shamaki ya ta’allaka matsalolin da aka samu lokacin gudanar da jigilar mahajjatan a kan wasu halaye na mahajjata masu azarbabi wadanda suke zuwa cibiyoyin tashin maniyyata tun kafin lokacin tashinsu ya yi, inda suke jawo a dauka an bar su yashe a cibiyoyin duk lokacin da jirgi ya tashi. Ya zargi wadanda suka saba zuwa aikin Hajji da rudin sababbin maniyyatan suna keta dokoki da ka’idojin da aka ajiye don kwashe mahajjatan. Sannan ya ce wani bangare na laifin yana wuyan jami’an alhazai na jihohi kan gaza daukar matakin da ya dace wajen ladabtar da irin wadancan daidaikun maniyyata, musamman kai-kawo dillalan-zaune wadanda suka sha alwashin lalata nasarorin da hukumar ta samu wajen aikin jigilar maniyyatan.
Ya ce, an samu korafe-korafe kan jinkirin tashin maniyyata daga Bauchi da Yola da kuma Legas, amma ya ce, jiragen da aka tura wadannan cibiyoyi sun hanzarta zuwa domin tabbatar da cewa an kwashe kowane maniyyaci zuwa Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin. A cewarsa, sashin sanya ido da tabbatar da bin ka’ida na hukumar ya gamsu da rawar da kamfanonin jiragen saman da Gwamnatin Tarayya ta ba su jigilar maniyyatan suka taka.
“Jigilar maniyyata aikin Hajji zuwa Saudiyya ta samu nasara, kamar bara. Kashi na farko galibi yakan fuskanci matsaloli saboda dalilai da dama, daya daga ciki jinkirin karbar kudin Hajji daga hukumomin jihohi da mika su ga hukumar domin biyan masu gudanar da aikin,” inji shi. Sai ya kara da cewa: “Kuma karin kudin kujera a bana ma ya jawo matsala ga aikin, amma saboda hukumar ta shirya sosai, sai aka shawo kan matsalolin nan da nan aka ci gaba.”
Shamaki ya ce, ma’aunin da aka yi amfani da shi wajen nuna an samu nasarar aikin ya ginu ne a kan cewa an samu nasarar kwashe mahajjatana dukansu duk da cewa an fara jigilar ce bayan mako daya da Saudiyya ta bude filayen jiragen samanta ga mahajjata. Ya ce wannan yana nufin an kwashe mahajjatan Najeriya dubu 79 zuwa kasa Mai tsarki a cikin mako uku. “Wannan babbar nasara ce,” inji shi.
Ya ce, aikin kwaso alhazan zuwa gida zai fi gudana cikin jin dadi, inda ya yi alkawarin cewa Hukumar NAHCON za ta tabbatar da cewa aikin ya tafi ne a kan salon “wanda ya fara zuwa shi zai fara komawa.” Sai ya yaba wa shugabannin hukumar kan tsare-tsare masu kyau da jagorancin da suke yi sai kuma sauran masu ruwa-da-tsaki kan hadin kan da suke bayarwa.