Wani matashi mai suna Ibrahim Elhoseny ya koma yin wasan kwallon Tebur da aka fi sani Tennis da baki maimakon amfani da hannuwansa.
Shi dai Ibrahim wanda dan aslain Masar ne ya rasa hannayensa tun yana dan shekara 10 a sanadiyyar wani hadari da ya rutsa da shi amma maimakon ya hakura da wasan Tennis da ya fi kauna a rayuwarsa sai ya yanke shawarar ya cigaba da amfani da bakinsa wajen rike katakon (paddle) da ake amfani da shi wajen yin kwallon tebur da bakinsa ba tare da matsala ba.
Ibrahim yakan yi amfani da kafafuwansa ne wajen jefa kwallo sama sannan ya yi amfani da baki wajen hankadata da karfi a lokacin da yake wasa.
Magoya bayansa da masu sha’awar wasan kwallon Tennis kan yi tururuwa don ganin yadda wannan bawan Allah ke amfani da baki wajen yin wasan kwallon Tennis. A mafi yawan lokaci filin kan rude da tafi da sowa wajen jinjinawa Ibrahim musamman ganin yadda yake ba masu lafiya kashi a lokacin da suke fafatawa da shi. Hakan ta janyo masa yin suna da daukaka a fagen kwallon Tennis inda ake gayyatarsa a gasar wasanni a ciki da wajen Masar.
A watan jiya ma Hukumar shirya wasan kwallon Tenni ta duniya ta gayyaci Ibrahim Elhoseny inda ya fafata a gasar kwallon Tennis ta duniya da ake wa lakabi da ZEN-NOH 2014 World Team Table Tennis Championship da ta gudana a Tokyo da ke Japan. Haka kuma Ibrahim ya haskaka a gasar kwallon Tennis ta yankin Afirka a shekarar 2011.
Babban burin Ibrahim a yanzu shi ne ya cigaba da nuna kwazo a fagen kwallon Tenni da hakan za ta ba shi damar wakiltar Masar a gasar Olamfik da za a yi nan gaba.
An samu mai wasan kwallon Tennis da baki bayan ya rasa hannayensa
Wani matashi mai suna Ibrahim Elhoseny ya koma yin wasan kwallon Tebur da aka fi sani Tennis da baki maimakon amfani da hannuwansa.Shi dai Ibrahim…