✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sallami ’yan kwallon Ribers United daga asibiti

A shekaranjiya Laraba ne aka sallami wasu daga cikin ’yan kwallon Ribers United daga asibitin da aka kwantar da su bayan motarsu ta yi hadari…

A shekaranjiya Laraba ne aka sallami wasu daga cikin ’yan kwallon Ribers United daga asibitin da aka kwantar da su bayan motarsu ta yi hadari a karshen makon jiya.  ’Yan wasan da aka sallama sun hada da Yusuf Ijaiyeola da Sope Hameed da kuma Kyaftin din kulob din Festus Austin.
Dukkan ’yan kwallon sun yi rauni ne a hadarin da ya rutsu da motar ’yar kwallon a kauyen Ndele da ke Jihar Ribas.  Bayan hadarin ne sai aka garzaya da su asibitin kwararru na Jami’ar Fatakwal don duba lafiyarsu.
Likitan kulob din Chukwumeka Agu ya bayyana cewa biyu daga cikin ’yan kwallon da aka sallama sun warke sarai kuma za su iya komawa fili don cigaba da yin kwallo.
“Yusuf ne kawai dan kwallon da ba zai iya cigaba da kwallo a halin yanzu ba, bayan ya samu rauni a cinyarsa”, inji shi.
Kafar watsa labaran wasanni ta SuperSport ta ce 17 daga cikin ’yan kwallon da hadarin ya rutsa da su ba su samu mummunan rauni ba, kuma tuni Likitoci suka duba lafiyarsu kuma aka sallame su nan take.
Tuni Hukumar NFF ta aika da sakon jaje ga kulob din ta hannun Shugaban Hukumar NFF na daya Seyi Akinwunmi, inda ta nuna alhininta a kan hadarin da ya rutsa da su.