✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sako mutum 10 aka yi garkuwa da su a jihar Kogi

An sako mutum 10 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa dasu a jihar Kogi makon da ya gabata. Jami’in hulda da jama’a na rundunar…

An sako mutum 10 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa dasu a jihar Kogi makon da ya gabata.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar Kogi, DSP William Aya, ne ya bayyana hakan ranar Talata a birnin Lokoja.

Wadanda aka sako din sun hada da: shida daga cikin ma’aikatan Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) wadanda aka sace su akan hanyar Obajana zuwa Kabba da kuma jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta NSCDC, wanda aka sace a garin Alo-Offoke da ke kan hanyar Itobe zuwa Ayingba.

Jami’in ya ce, an sako ma’aikatan hukumar JAMB dinne da karfe 12 na daren ranar Litinin wadanda tuni an garzaya dasu garin Abuja da safiyar ranar Talata.

Ya kuma tabbatar da sako jami’an tsaron NSCDC a ranar Lahadi kuma tuni aka mika su ga iyalansu.

Mai Magana da yawun ’yan sandan bai yi karin bayani ba akan ko an biya wasu kudade kafin a sako mutanen ba.

An dai yi garkuwa da jami’an tsaron na NSCDC dinne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Makurdi babban birnin jihar Benuwe, saboda hallartar wata jarabawar aiki, yayin da su kuma ma’aikatan na hukumar JAMB an sace su ne a hanyarsu ta zuwa Kwara saboda aikin sanya ido a kan shirye-shiryen Jarabawar cancantar shiga makarantun gaba da sakandare ta UTME.