✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An saki Yahaya Bello bayan cika sharuɗɗan beli

An saki Yahaya Bello bayan cika sharuɗɗan belin. An sake shi da yammacin yau Juma’a.”

An saki tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello daga gidan yarin Kuje bayan ya cika sharuɗɗan belin da babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama, Abuja ta gindaya.

Mai magana da yawun Hukumar gidan yari na ƙasa reshen babban birnin tarayya Abuja, Adamu Duza ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yammacin ranar Juma’a.

Duza ya ce, “An saki Yahaya Bello bayan cika sharuɗɗan belin. An sake shi da yammacin yau Juma’a.”

“Kwanturola na hukumar gidan yarin na Abuja, Ajibogun Olatubosun, yana sane da umarnin don tabbatar da sakin sa kuma an cika dukkan sharuɗɗan.”

Mai shari’a MaryAnne Anenih ce ta bayar da belin Yahaya Bello a ranar Alhamis a kan kuɗi N500m.

Sharuɗɗan sun haɗa da gabatar da mutum uku, kowanne wanda ya mallaki kadarori a wasu wurare masu daraja a Abuja, kamar unguwannin Maitama, Guzape ko Asokoro.

Kotun ta kuma umurci Bello da ya miƙa fasfo ɗinsa tare da hana shi fita wajen Najeriya ba tare da izini ba.

Tsohon gwamnan tare da Shuaibu Oricha da Abdulsalam Hudu, suna fuskantar tuhume-tuhume guda 16 da suka haɗa da: haɗa baki da cin amana da mallakar kadarori ba bisa ƙa’ida ba, wanda hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa EFCC ta gabatar.

Dukkansu ukun sun musanta aikata laifin da ake tuhumarsa.

Mai shari’a Anenih ta ƙi amincewa da buƙatar belin Bello tun a farko kan wasu dalilai, amma ta bayar da belin waɗanda ake tuhumar.

An amince da sabuwar buƙatar Bello a ranar Alhamis, wanda ya kai ga sakin shi.